Queen Elizabeth: Sarauniyar Ingila ta gama shiri tsaf domin mikawa Yarima mai jiran gado karagar mulki

Queen Elizabeth: Sarauniyar Ingila ta gama shiri tsaf domin mikawa Yarima mai jiran gado karagar mulki

- Rahoto ya nuna cewa, Yarima Charles na gab da karbar akalar masarautar Birtaniya

- Hakan zai biyo baya ne idan sarauniyar ta cika shekaru 95 a duniya kuma ta yi murabus

- Badakalar da ta taso tsakanin Andrew da Epstein ta kara tabbatar da yadda yariman zai tafi da masarautar

Rahotanni sun nuna cewa, yarima Charles na shirye-shiryen hayewa karagar mulkin masarautar Birtaniya, a lokacin da sarauniya ta cika shekaru 95 a duniya.

Babban dan sarauniyar, ya hadu da mahaifinsa a Sabdringham a ranar 26 ga watan Nuwamba, don tattaunawa a kan yadda dan uwanshi ya bayyana dangartakarshi da Jeffry Epstein.

Rawar da Yarima Charles ya taka wajen sa Yarima Andrew ya yi murabus, ya tabbatar da zargin da ake na cewa zai zama yarima mai jiran gado, wanda hakan zai bashi damar juya al’amuran gidan sarautar yayin da mahaifiyarshi zata zauna a sarauniya.

KU KARANTA: To fah: Budurwa ta kashe kanta awanni kadan bayan saurayinta yayi hatsari ya mutu

Nan da watanni 18 ne sarauniya Elizabeth zata cika shekaru 95 a duniya. A shekaru 95 ne maigidanta Yarima Philip ya yi murabus daga lamurran sarautar.

Wata maijya daga gidan sarautar ta bayyana cewa: “Badakalar da ke tsakanin Andrew da Epstein ce ta ba wa Charles damar bayyana cewa zai iya rike masarautar. Babu wanda yafi karfin gidan sarauta. Ko Andrew, dan da sarauniyar tafi so a duniya."

“Charles ya yi duk yadda ya dace, kamar dai yadda Sarki ke yi. A don haka ne nan ba da dadewa ba zai zama. A wannan lokacin ne Charles zai taso a matsayin sarkin maijiran gado.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel