Tirkashi: Miji ya bayyana yadda ya kama matarshi tana lalata da dan uwanshi na jini

Tirkashi: Miji ya bayyana yadda ya kama matarshi tana lalata da dan uwanshi na jini

- Wani dan kasuwa a jihar Ibadan ya sanar da kotu yadda matarshi ke lalata da kaninshi duk in yayi tafiya

- Ya ce, ba sau daya ko sau biyu ba mahaifinshi ya kamata da kanin nashi da ke binshi

- Hakan kuwa ya kawo tarin matsaloli gareshi daga danginshi bayan da yaki rabuwa da ita

Wani dan kasuwa a jihar Ibadan mai suna Saheed Eniola, ya sanar da wata kotu da ke jihar Ibadan yadda aka dinga kama matarshi mai suna Kafayat, da kaninshi suna cin amanarshi.

A ranar Litinin, ya sanar da yadda wannan mummunar alakar da ke tsakanin matarshi da kaninshi ta dinga kawo tashin hankula a danginsu.

Saheed ya sanar da hakan ne yayin da yake mayar da martani a kan karar da Kafayat ta kai gaban kotu don neman saki. Chief Ademola Odunade ne ya shugabanci shari’ar.

“Dalilin da yasa na aminta da bukatar Kafayat na raba aurenmu shine, ita shaidaniya ce kuma ta wargaza mana dangi saboda rashin kamun kanta.

“Duk lokacin da na tafi balaguron kasuwancina, mahaifina yana kama Kafayat da kanina da ke bina; duk da ja mata kunne da yake yi, Kafayat ta cigaba da yaudarar kanina don cin amanata.

“Mahaifina ya yi barazanar sallama ni matukar ban koreta ba. Duk da wannan matsalar, ban dena sauke hakkin ‘ya’yana biyu ba da ke kai na. Kawai dai na dena zama tare da Kafaya,” ya sanar da kotun.

KU KARANTA: Naira dubu dari bakwai ake biyana fansho duk watan duniya - Tsohon gwamna

Saheed ya kara da cewa, matarshi ta dade tana tsine mishi, lamarin da yake kaawo mishi lalacewar harkar kasuwancinshi.

“Na roki Kafaya da ta bani yarana amma ta ki; akwai yuwuwar ta bata musu tarbiya,” Saheed ya ce.

A bangaren Kafaya, ta bayyana yadda mijinta ya dena rayuwa tare dasu tun shekaru 12 da suka gabata. Yaranta kuwa ita take kula dasu. Ta ce ya bukaci ta bashi yaran, amma ta hana saboda tsoron ba zai sa su makaranta ba.

Amma kuma ta ki mayar da martani a zargin cewa tana lalata da kaninshi. Kotun ta bukaci a kawo danginshi don su zama shaida. Ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel