Allah ya yi wa wani tsohon dana majalisar dokokin tarayya rasuwa

Allah ya yi wa wani tsohon dana majalisar dokokin tarayya rasuwa

A jiya Laraba ne kakakin majalisar dokokin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya sanar da rasuwar wani tsohon dan majalisar, Tony Okey.

Gbajabiamila ya sanar da hakan ne a zaman zauren majalisar. Ya ce Tony Okey yana daga cikin 'yan majalisar dokokin kashi na hudu a Najeriya. Ya tabbatar da cewa, Okey ya bautawa tare da hidimtawa kasar nan ba tare da son kansa ba a lokacin da yake majalisar.

Ya yi wakilci a majalisar ne tsakanin 1999 da 2003.

Kamar yadda ta kasance al'adar majalisar, an yi shirun minti daya don girmama tsohon dan majalisar, kuma an hada da yi masa addu'ar rahamar Ubangiji.

DUBA WANNAN: Tirkashi: An cafke wata mata dauke da ATM 23 boye a 'gabanta'

A wani cigaba kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa, wani tsohon sanata, Emmanuel Onwe daga jihar Ebonyi, tsohon kakakin majalisar jihar Bayelsa, Friday Komboyein da wasu mutane hudu an gurafanar da su gaban kotun manyan laifuka ta musamman a Abuja, a kan zarginsu da ake da karantsaye ga dokokin aiyukan gwamnati.

Wata takardar da kakakin kotun laifuka na musamman, Ibraheem Zakariya ya fitar, ya ce an gurfanar da tsohon kwamishinan jihar Ebonyi ne sakamakon kin mika takardar bayyana kadarorinshi a lokacin da ya dace. An gurfanar da Komboyein ne da sauran a kan zarginsu da ake da amfani da kujerarsu ba ta yadda ya kamata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel