Masu garkuwa da mutane sun sace babban hakimi a babban birnin tarayya Abuja
Wasu gungun miyagu yan bindiga sun yi awon gaba da Alhaji Mohammed Ibrahim Pada, hakimin garin Rubochi na karamar hukumar Kuje dake babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga sace hakimin, yan bindigan sun raunata yaran hakimin guda biyu bayan sun sassaresu da adda a yayin da yaran suka yi kokarin ceto mahaifin nasu daga hannun barayin.
KU KARANTA: Rikicin duniya da mai rai ake yin ta: Miji ya zargi matarsa da kwanciya da maigidansu
Wani mazaunin garin daya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 2 na daren Laraba, inda yace yan bindigan sun shiga garin ne dauke da muggan bindigu, sa’annan suka kutsa kai cikin gidansa, suka daukeshi.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa jin karan harbe harben yasa yaran hakimin guda biyu suka yi kan yan bindiga da nufin kwato babansu, amma sai wani dan bindigan ya dauki adda ya sassara yaran duka, nan suka fadi cikin jini.
Majiyar ya bayyana cewa a yanzu haka jama’an garin suna cikin zaman dardar, sa’annan yace yan bindigan sun tuntubi iyalan hakimin da misalin karfe 8:14 na safiyar Laraba, hatta hakimin ya yi magana da iyalansa, amma dai basu nemi ko sisi a matsayin kudin fansa ba.
Daga cikin sarakunan gargajiyan da suka fara garzayawa gidan hakimin akwai sarakunan Gwargwada, Ugbada, Alhaji Hassan Agabi, da kuma Etsu Yaba, Alhaji Adamu Abdullahi, inda suka isa gidan domin jajanta ma iyalansa.
Ita ma kaakakin rundunar Yansandan Abuja, Maryam Yusuf ta tabbatar da satar hakimin, amma tace suna ta kokarin ceto shi da ransa cikin koshin lafiya, sa’annan ta bada tabbacin kamo barayin.
A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun yi awon gaba da injiniyoyi guda 3 yan kasar China dake aiki a wani sansanin hakar ma’adanan kasa dake yankin Itagunmodi na jahar Osun, bayan sun kashe wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya.
Wani babban jami’in tsaro a jahar Osun daya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa baya ga yan kasar China guda uku da yan bindigan suka sace, sun bindige wani daban a yayin da yayi kokarin tserewa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng