Kaf kabilun Najeriya babu masu wulakanta matansu kamar Hausawa - Rabi Salisu

Kaf kabilun Najeriya babu masu wulakanta matansu kamar Hausawa - Rabi Salisu

- An bayyana Malam Bahaushe a matsayin mutumin da yafi iya tozartawa tare da cin zarafin mata a kabilun kasar nan

- Babban abun mamakin shine, yadda Bahaushe ke tara mata hudu tare da yara birjik inda daga baya yake turasu almajiranci

- Hajiya Rabi ta ce, da yawa daga cikin ‘yammatan da suka fada harkar karuwanci suna yin hakan ne saboda tsabar talauci

An bayyana Bahaushe a matsayin mutumin da yake tozartawa tare da cin zarafin mata da sunan aure, a tsakanin sauran kabilun kasar nan baki daya.

Shugabar cibiyar Arridah Foundation dake Kaduna, Hajiya Rabi Salisu Ibrahim ce ta bayyana hakan. Ta sanar da hakan ne yayin tattunawa da manema labarai dangane da batun dokar haramta karin aure da mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya gabatar a birnin Kano.

Hajiya Rabi ta cigaba da cewa, babban abun mamaki ya kare a kan Bahaushe, wanda shi a rayuwarshi babu abinda ya tsare illa batun kara aure, ya tara mata hudu a gidan haya, ga talauci. Yayin da iyali suka yi yawa sai a fara neman wajen saka su. Karshen lamarin sai a mikawa Malamin allo da sunan almajiranci, babu batun tarbiyya.

Shugabar cibiyar Arridah din tace, lallai ya zama wajibi ga dukkan wani mai hankali da ya goyi bayan wannan kudiri da mai martaba ya bijiro dashi. Domin hakan zai tabbatar da daraja tare da kare kimar kasar Hausa.

KU KARANTA: Ragon maza: Magidanci yayi yaji ya bar matansa guda hudu saboda rigimar su

Hajiya Rabi ta soki wani hadisi da hausawa ke dogaro dashi. Suna cewa bakin da Allah ya tsaga, baya hana shi abinci. Ta ce wannan ya ci karo da tsarin rayuwa. Domin Allah bai yarda ka dauko nauyin da ba zaka iya saukewa ba. Ta kara da shawartar jama’ar kasar hausa dasu guji kawo cikas a duk inda aka bijiro da wani batu na cigaba, musamman a kan abinda ya shafi cigaban mata.

Hajiya Rabi ta soki lamarin rubuce-rubucen da wasu hausawa masu adawa da batun sarkin Kano ke yi. Su kan sokeshi a kafafen sada zumuntar zamani da cewa, da zina cikin wadata gara aure cikin talauci. Tace hakan ba gaskiya bane, saboda wasu ‘yan matan kan fada mummunar harkar zina ne saboda talauci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel