Ragon maza: Magidanci yayi yaji ya bar matansa guda hudu saboda rigimar su

Ragon maza: Magidanci yayi yaji ya bar matansa guda hudu saboda rigimar su

- Wani magidanci mai suna Malam Rabiu, mai mata hudu ya bayyana irin cin zarafin da ya fuskanta daga matanshi

- Saboda hakan ne ya tattara komatsanshi ya garzaya Kano daga jihar Benuwe da sunan yaji

- ‘Yar uwarshi da ya sauka a wajenta a Kano, ta ce ba zai koma ba har sai matan nashi sun gane kuskurensu

A yayin da ake bikin ranar cin zarafin mata ta duniya, wani magidanci ya bayyana yadda matanshi ke cin zarafinshi.

Magidancin mai suna Malam Rabiu ya bayyana yadda matan sa har hudu ke hade kansu wajen cin zarafinshi

Yace ya yi yaji ne tun daga garin Katsina Ala a jihar Benuwe zuwa wajen ‘yar uwarshi dake a nan Kano, mai suna Asma’u Muhammad.

Wakiliyar gidan rediyon freedom da ke Kano ta zanta da wannan magidanci, wanda ya bayyana mata yadda wannan lamarin ya kasance.

Malam Rabiu ya kara da cewa, wannan lamarin na yajin maza ba sabon abu bane a wajen maza. Yace bacin rai da yake samu a wajen matanshi ko wacce rana ya sa shi wannan yaji.

KU KARANTA: Rahama Sadau: Dalilin da yasa bana mayar da martani ga masu zagi

Daga karshe ‘yar uwar magidancin, Asma’u Muhammad, wacce ya gudo wajenta a Kano, ta bayyana yadda lamarin ya faru, inda tace zasu mayar da magidancin dan uwanta gida amma sai matan sun gyara kura-kuransu.

Yaji dai a al’adar kasar hausa, halayya ce ta mata. Matan kan yi yaji ne a duk lokutan da wani rikici ya ratsa tsakaninsu da mazansu kuma an yi kokarin sulhu amma abin ya gagara.

Sau da yawa idan matan suka yi yaji, mazan kan garzaya inda suka je don yin biko. Daga can ne za a zaunar dasu don yi musu sasanci a kan mataslar da suka kasa shawo kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel