DSS ta kama hatsabibin mai garkuwa da mutane da ya sace alƙalin kotun daukaka kara

DSS ta kama hatsabibin mai garkuwa da mutane da ya sace alƙalin kotun daukaka kara

Hukumar jami’an tsaro na farin kaya, sun cafke Stanley Onoriode Ekemaye, wanda aka kwatanta da “Hatsabibin mai garkuwa da mutane” wanda ake zargi da shirya garkuwa da Chioma Nwosu-Iheme, alkalin kotun daukaka kara na reshen jihar Benin.

An yi garkuwa da Nwosu ne a ranar 30 ga watan Oktoba, bayan da aka bi ta a baya daga titin Benin-Agbor. An tsareta ne kusa da wata coci da ke yankin.

An hallaka dan sandan da ke tsaron lafiyarta a take. Ta kuma samu yancinta ne bayan makonni biyu.

Jaridar The Cable ta gano cewa, an cafke Ekemaye ne a sa’o’in farko na ranar Talata, a Okwuzi Egbema a karamar hukumar Ogba/Egbema/Ndonu da ke jihar Rivers.

An gano cewa, Ekemaye ya dade yana shirya fashi da makami tare da garkuwa da mutane a jihohin Delta, Edo da Rivers na shekaru 6.

DUBA WANNAN: EFCC ta bankado laifin sanatan da ke son a kirkiri dokar amfani da dandalin sada zumunta

Daga cikin wadanda ake zargin yayi garkuwa dasu akwai Francisca Okhiria, manajan daraktar kamfanin jiragen kasa na Najeriya, wacce aka yi garkuwa da ita a ranar 14 ga watan Satumba kuma aka sake ta bayan makonni uku.

Sauran sun hada da Esther Achimogu da Elias Ovesour wadanda aka sace a watan Yuni. Akwai Elizabeth Mekuye, sirikar Ifeanyi Okowa, Gwamnan jihar Delta, wacce aka sace a watan Augusta kuma aka sake ta a watan Satumba

Sylvanus Okogbenin, shugaban asibitin kawararru na Irrua da aka sace a ranar 26 ga watan Augusta. Hakan kuma ya yi ajalin jami’an ‘yan sanda biyu. Duk ana alakanta wannan ta’asar da Ekemaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel