Jami’an EFCC sun yi ram da shugaban kurkukun Kirikiri da babban likitan kurkukun
Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da kama shugaban gidan yarin Kirikiri dake jahar Legas, Emmanuel Olaniyi tare da babban likitan kurkukun, Hemeson Edson Edwin da hannu cikin tafka laifin cin hanci da rashawa.
Kaakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya EFCC ta kama mutanen biyu da ne saboda hada baki wajen bayar da shaidar rashin lafiya na bogi ga wani gawurtaccen dam damfara da aka yanke ma hukuncin shekaru 24 a kurkukun, wanda ya bashi daman fita da sunan zuwa wani asibiti, daga nan ya sake kulla wata damfarar daya samo dala miliyan 1.
KU KARANTA: Jiya ba yau ba: Gwamna Masari ya bada labarin yadda Buhari ya shiga aikin Soja
Kaakakin EFCC yace mutanen biyu sun baiwa hukumar muhimman bayanai game da rawar da suka taka wajen baiwa dam damfara Hope Olusegun Aroke daman fita daga kurkukun kirikiri ya je ya tafka ta’asarsa.
“Aroke na daga cikin wasu yan Najeriya biyu dake kasar Malaysia wanda EFCC ta kamasu a karshen shekarar 2012 a unguwar Victoria Island Legas. Aroke dan asalin garin Okenen jahar Kogi ne, amma ya yi ikirarin yana karatu ne a jami’ar kasar Malaysia.
“Sai dai bincikenmu ya nuna mana cewa Aroke ne shugaban wata katafriyar kungiyar yan damfara da suka karade nahiyoyin duniya guda biyu, bayan mun kamashi, mun gudanar da bincike a gidansa inda muka gano kwamfutocin tafi da gidanka, takardun tafiye tafiye, manyan motoci 3 da na’urorin sadarwa daban daban.
“Daga bisani mai sharia Lateefa Okunnu ta babbar kotun jahar Legas ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 12 ga kowanne laifi cikin laifuka biyu da ake tuhumarsa dasu da suka shafi yaudara, hada takardar cire kudi na bogi, da kuma satar kudi ta yanar gizo.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng