Rufe iyakokin Najeriya: Obasanjo ya bayyana matsayarsa, ya gargadi kasar Benin

Rufe iyakokin Najeriya: Obasanjo ya bayyana matsayarsa, ya gargadi kasar Benin

A ranar Talata ne tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bukaci kasar Benin, mai makwabtaka da Najeriya, da ta canja yadda take gudanar da wasu al'amuranta matukar tana son gyara dantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da yake gana wa da manema labarai a Addis Ababa, inda yake halartar wani taro na kwanaki biyu a kan sabuwar yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin kasashen Afrika (AfCFTA) da aka kulla.

An shirya taron ne domin tattauna wa a kan sabuwar yarjejeniyar AfCFTA da kasashen nahiyar Afrika suka kulla domin inganta harkokinsu na kasuwanci da bunkasa tattalin arziki.

Kungiyar kasashen nahiyar Afrika (AU) tare da hadin gwuiwar bankin cigaban nahiyar Afrika (AfDB) da kuma bankin AFREXIMBANK, sune suka dauki nauyin shirya taron.

A cewar Obasanjo, kasar Benin ta yi kaurin suna wajen karya doka da saba wa yarjejeniya, halayen da ya ce sun dade suna illata tattalin arzikin Najeriya.

DUBA WANNAN: Zaben Bayelsa: Jonathan ya mayar wa da Sule Lamido martani

"Ta taba faruwa lokacin da nake shugaban kasa a Najeriya. Na kira shugaban kasar Benin a wancan lokacin, Nicephore Dieudonne Soglo, domin mu hadu mu tattauna a kan yanayin aikin jami'an tsaro a kan iyakokin kasashenmu.

"Daga bisani mun hadu a Badagry da ke Najeriya, inda muka kulla yarjejeniyar cewa Najeriya zata jibge jami'an hukumar kwastam a kasar Benin.

"Har yanzu Najeriya tana da jami'an kwastam a Benin. Bamu da matsala da kayan da kasar Benin ke kera wa ko sarrafa wa - muna maraba da su.

"Amma matukar kasar Benin zata bar kasarta ta zama jujin zubar da kowanne irin kaya, zasu cigaba da samun matsala da Najeriya," a cewar Obasanjo.

Obasanjo ya yi kira ga shugabannin kasashen Afrika da su mayar da hankali wajen tabbatar da ganin cewa yarjejeniyar da suka kulla ta fara aiki, ba ta tsaya iya maganar baki ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel