Kananan ƙasashe 10 da ba kowa ya san su ba

Kananan ƙasashe 10 da ba kowa ya san su ba

Akwai sama da kasashe 200 a duniya. Amma kuma akwai kananan kasashe da yankuna na duniya da bamu taba saninsu ba. Sun mamaye karamin yanki ne kuma wasu daga cikinsu ba zasu iya daukar mutane masu yawa ba.

Ga jerin sunayen kasashe kanana 10 na duniya da suke da mutanen da basu wuce yawan birni daya ba ko kuma karamin kauye.

1. Palau

Jamhuriyar Palau kasa ce guda amma a tsibiri. Ta kunshi tsibirak 300 mabanbanta a girma. Palau na da mutane 21,347. Tana da tsirrai kala-kala tare da tsuntsaye. Ruwan da ke zagaye da tsibirin kuwa na da nau'ika 130 na kifaye masu muguwar barazana.

2. Niue

Niue karamin tsibiri ne a Oceania. Duk da kyan tsarin kasar, masu yawon bude ido basu santa ba. Saboda haka ne kasar ta dogara da taimakon kasashen ketare kamar New Zealand.

Babban birnin jihar karamin kauye ne mutane 600. Tsibirin yana da filin sauka da tashin jiragen sama da kuma babbar kasuwa.

3. Saint Kitts and Nevis

Kasar na da tsibirai biyu ne: Saint Kitts da Nevis. Abinda ke taka rawar gani wajen habaka tattalin arzikin kasar shine yadda duk wanda ya mallaki a kalla $250,000 da zai saka a masana'antar sukarin kasar ake bashi shaidar zama dan kasa. Za a iya samun shaidar zama dan kasar kuma ta hanyar siyan kadara ta a kalla $400,000 a kasar.

4. The Principality of Hutt River

Wannan matsakaiciyar kasa ce da ke yanki daya da Australia. Leonard Casley ne ya kirkiro kasar yayin da ya bayyana gonarsa ta zamo sabuwar kasar. Duk da kasar bata karkashin kowacce kasa, ta na da kudinta, hatimi da kuma fasfoti. A wani yankin kasar, masu yawon bude ido na ganin masarautar mai girma yarima Leonard I na Hutt.

5. Tuvalu

Tuvalu na daya daga cikin kanana kuma fatararrun kasashe a duniya. Da ace kasar ba ta yanar gizo da TV wadanda suke samar mata da kudin shiga, da fatarar tafi haka kamari.

DUBA WANNAN: EFCC ta bankado laifin sanatan da ke son a kirkiri dokar amfani da dandalin sada zumunta

6. Nauru

Itace kasa mafi kankanta mai cin gashin kanta kuma tsibiri a wannan duniyar tamu. Nauru bata da babban birni ko kuma wani sufuri na gwamnati. Matsalar muhalli ce ta sa ba a san kasar ba. Wani abu gane da kasar shine yadda mafi yawan 'yan kasar ke da muguwar kiba.

7. The Principality of Seaborga

Matsakaiciyar kasar da ke yankin Italia ta samu shugabancin mai martaba Marcello na daya ne. Kasar kauye ce da kusa da iyakar kasar Faransa. Tana da rundunar sojin da ta kunshi mutane uku: Ministan tsaro da masu gadin iyakar kasar mutane biyu.

8. The Republic of Molossia

Jamhuriyar Molossia madaidaiciyar kasa ce da Kevin Baugh ya kirkira. Tana nan a Nevada da ke Amurka. Masu rayuwa a kasar sun kunshi Baugh, iyalansa, karnikansa 3, magensa 1 da zomonsa 1. Molossia na da take kasa da tutarta. Akwai kuma hukuncin kisa ga manyan laifuka.

9. Sovereign Military Oder of Malta

Baya da birnin Vatican, akwai wata karamar kasa da ke yankin Rome, wacce ake kira da Sovereign Military Order of Malta. Tana da gine-gine uku, biyu suna Rome sai daya a tsibirin Malta. Kasar na da kudinta, hatimi, lambar motoci da fasfoti.

10. The Principality of Sealand

Kasa ce da take da nisan mil 6 tsakaninta da Birtaniya. Yarima Regent ne ke shugabantar kasar. Ana iya siyan sarauta daga kasar da fam kadan ta adireshin yanar gizonta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel