Wata Uwa ta halaka dan cikinta bayan ta hankada shi a cikin rijiya

Wata Uwa ta halaka dan cikinta bayan ta hankada shi a cikin rijiya

Rundunar Yansandan jahar Osun ta sanar da kama wata mata mai suna Rukayat Abulraheem mai shekaru 33 a garin Osogbo, babban birnin jahar Osun biyo baya zarginta da ake yi da halaka dan cikinta.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito har yanzu babu tabbataccen hujja da uwar ta bayar na aikata ma dan da ta haifa wannan aika aika, amma Yansanda sun bayyana matar ta kashe Abdulganiyu ne a ranar 17 ga watan Nuwamba ta hanyar hankada shi cikin rijiya.

KU KARANTA: Kowa ya bar gida, gida ya bar shi: Atiku zai dawo Najeriya ranar da ya cika shekaru 73

Sai dai bayan Yansanda sun kamata, sun gudanar da bincike a kanta, sa’annan suka gurfanar da ita gaban kotu a ranar Juma’ar da ta gabata, amma a yayin zaman kotun, sai lauyanta, Galadima Adeoye ya bukaci Yansanda su je su sake gudanar da bincike yadda ya kamata.

Amma ba tare da bata lokaci ba, Dansanda mai shigar da kara, Wale Fatoba ya nuna bacin ransa game da maganan da lauyan ya yi, inda ya bayyana ma kotu cewa sai da suka gudanar da cikakken bincike a kan Rukayat kafin ma su gurfanar da ita.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, dai Alkalin kotun, mai sharia Olusegun Ayilara ta bada umarnin cigaba da garkame Rukayat a hannun Yansanda zuwa ranar 4 ga watan Disamba da za’a fara shari’ar ganga ganga.

A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Ogun ta sanar da kama wata mat yar shekara 42 mai suna Temitope Akinola biyo bayan zarginta da ake yi da kwankwada ma jaririyar diyarta fiya fiya bayan kwanaki biyu kacal da haihuwarta.

Yansanda sun ce mahaifiyar jaririyar ta bar jaririyar ne a hannun kulawar babarta, inda ta shiga bandaki domin ta yi wanka, amma koda ta dawo, sai dai kawai ta tarar da gawar diyar kwance ba rai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel