Jonathan ya yi musayar nasarar PDP a Bayelsa - Zauren dattawan PDP

Jonathan ya yi musayar nasarar PDP a Bayelsa - Zauren dattawan PDP

- Zauren dattawan jam’iyyar PDP sun yi ikirarin cewa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi musayar nasarar PDP ne a zaben gwamnan jihar da ya kammala

- Shugaban zauren dattawan, Chief Benson Odoko, ya lissafo take-taken tsohon shugaban kasar a matsayin hujjar ikirarinsu

- Kamar yadda Odoko ya ce, yakamata a hukunta Jonathan a kan zarginsa da ake da cin amanar jam’iyyar a jihar Bayelsa da Najeriya baki daya

Wata kungiya da ake kira da zauren dattawan PDP, ta zargi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, da musayar nasarar jam’iyyar a zaben 16 ga watan Nuwamba da aka yi a jihar Bayelsa.

Kamar yadda jaridar Daily Sun ta ruwaito, shugaban kungiyar, Chief Benson Odoko, a wata takarda ya zargi Jonathan da hada kai da shuwagabannin jam’iyyar APC a jihar.

Odoko ya yi ikirarin cewa, babu ko shakka tsohon shugaban kasar ya ci amanar jam’iyyar da ta kaishi matsayin mataimakin gwamna, gwamna, mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban kasar Najeriya baki daya.

DUBA WANNAN: Dankari: Matashi ya fito takarar kujerar shugaban mata a Kwankwasiyya

Ya danganta ziyarar da tsohon shugaban kasar ya kaiwa shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja, da babbar alamar da ta nuna yana wa APC aiki ne a maimakon jam’iyyarsa. Ya kara da cewa, Jonathan ya nisanta kansa daga shirye-shiryen jam'iyyar gabanin zaben gwamnan.

Ya kara da cewa, Jonathan da uwargidansa sun sadaukar da otal din Aridolf ga jiga-Jigan APC don taro tare da zaben fidda gwani.

Odoko ya kushe ziyarar da shuwagabannin APC na jihar da suka hada daTimpre Sylva, David Lyon da sauran ‘yan APC suka kaiwa Jonthan a Otueke.

Yace, dukkan wadannan take-taken na nuna cewa Jonathan ya ci amanar jam’iyyar da ta bashi damar da ba kowa ya samu ba a kasar nan.

Odoko ya bukaci shugabancin jam’iyyar da ya tattaro duk wani hukunci da yakamata Jonathan ya fuskanta a rawar da ya taka wajen kada jam’iyyar a jihar, da kuma fitowa fili da yayi yana murnar nasarar da abokan hamayya suka yi a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel