An samo yara guda 8 da mata masu ciki 14 a wani kamfanin haifar jarirai a jihar Abia

An samo yara guda 8 da mata masu ciki 14 a wani kamfanin haifar jarirai a jihar Abia

- Hukumar ‘yan sandan jihar Imo ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kafa cibiyar siye da sayar da jarirai

- Asirinsu ya tonu ne bayan da suka yi wa wata mata aiki suka cire ‘yan biyu tare da yin awon gaba dasu

- An gano mata masu ciki 14 da kananan yara 4 a gidan amma mamallakiyar cibiyar ta tsere

Hukumar ‘yan sandan jihar Imo, ta cafke wasu mutane biyu da take zargi da kafa wajen samar da jariran siyarwa a Aba, jihar Abia.

Kamen ya biyo bayan wani bin diddigin wata mata da jami’an ‘yan sandan suka yi. Sun zargi matar mai suna Blessing Sunday mai shekaru 30 a duniya, da ke aiki da wani gidan taimako da ke Umumkpee da taimakawa masu cibiyar. An zargeta da jan wata mata mai suna Onuwa Grace Nwachukwu, mai cikin ‘yan biyu zuwa gidan.

An yi wa matar aiki tare da ciro jariran. Mai cibiyar siye da siyar da jariran, Mma Achumba ta sace ‘yan biyun tare da siyar da su. Ita kuma Blessing ta hanzarta maida Grace zuwa kauyensu da ke Okwe-Owerre Umueze II amma tana ta zubar da jini.

A fusace, matasan kauyen suka kama Blessing zasu konata tare da gidan iyayenta, amma rundunar ‘yan sandan da suka je kauyen ne suka tseratar dasu.

KU KARANTA: Magani a gonar yaro: Amfani guda 11 da gwaza da ganyenta suke yi a jikin dan adam

‘Yan sandan sun gaggauta garzayawa da Grace asibitin ‘yan sanda dake Owerri inda aka kwantar da ita don bata kulawa.

An gano cewa, bayan an sallameta daga asibitin ne ta yi wa ‘yan sanda jagora zuwa cibiyar siye da sayar da jariran. An gano mata masu ciki 14 da yara kanana 4.

An aje matan ne a cibiyar ana jiran lokacin da zasu haihu a karbi jariran. Mai cibiyar kan biyasu kudi daga N300,000 zuwa N500,000. Hakan ya danganta da jinjiran mace ne ko namiji.

Daraktar kungiyar, Mma Achumba da ma’aikatanta sun tsere amma jami’an ‘yan sanda na ta kokarin gano inda suke don cafkesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng