An zo gurin: Zan cire duk wani jami'in kwastan da yake samun kudi fiye da albashin sa - Hameed Ali
- Shugaban hukumar kwastam ta kasa yayi alkawarin korar duk jami’in da aka kama da laifin rashawa
- Yace hukumar ba zata kyale duk jami’in da ta gano yana rayuwa da abinda ya fi karfin albashinshi ba
- Ya tabbatar da cewa, albashin ma’aikatan da hukumar ke biyansu ya ishesu rayuwa in sun tsarata
Col. Hameed Ali, shugaban hukumar kwastam na kasa ya yi alkawarin fatattakar duk wani jami’in hukumar da ba zai iya dogaro da albashinshi ba, kuma aka kamashi da laifin tara dukiya ta hanyar da ba halas ba.
Ali ya bada wannan jan kunnen ne yayin da yake kawata jami’an hukumar da aka karawa girma a Abuja a ranar Juma’a.
Cikin kwanakin nan ne hukumar ta karawa jami’ai 2,508 girma zuwa matsayi daban-daban. Ta kara da nada wasu jami’ai uku na hukumar a matsayin a mataimakan shugaban hukumar.
Shugaban kwastam din ya ja kunnen jami’an a kan rayuwa cikin wadaka da abinda ya fi albashinsu in har suna son cigaba da aiki da hukumar.
Kamar yadda yace, kowanne jami’i zai iya rayuwa a kan albashin da hukumar ke biyanshi, in ya tsara rayuwarshi da kyau.
KU KARANTA: Magani a gonar yaro: Amfani guda 11 da gwaza da ganyenta suke yi a jikin dan adam
“Zan nuna wa duk wani jami’i mafita, matukar ya ce ba zai yi rayuwa da albashinshi ba kuma zai dogara da haramtattun hanyoyi. Nasan hukumar na baku isasshen abinda zai isheku, kawai tsarin rayuwa ne babu. Zaku iya samun duk abinda kuke so,” ya shawarcesu.
Ya shawarcesu da su yi aikinsu kamar yadda ya dace. Ya bukacesu da su rungumi sabbin tsare-tsaren da hukumar ta zo dasu.
David Chikan, mataimakin shugaban hukumar, wanda ya yi jawabi a madadin duk jami’an da aka karawa girma, ya mika godiyarsu ga hukumar a kan karin girman. Chikan ya tabbatar da cewa ba zasu ba hukumar kunya ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng