Allah mai iko: Mace ta farko a duniya makauniya kuma kurma da ta zama likita

Allah mai iko: Mace ta farko a duniya makauniya kuma kurma da ta zama likita

- Alexandra Adams, budurwa ce mai shekaru 25 da ke shekara ta hudu a bangaren karatun likitanci, zata zama likita ta farko makauniya kuma kurma

- Alexandra ta ce abokan karatunta na tantamar ko zata iya aikin likitancin amma marasa lafiya na jinjinawa hazakarta

- An taba maida budurwar mai shekaru 25 gida bayan da aka turata wani asibiti don koyon makamar aiki, amma babban likitan ya ce ba zata iya ba

A lokacin da mutum ke son cimma wata manufa, babu wani kalubale da zai iya kawo mishi cikas. Alexandra Adams, budurwa mai shekaru 25 dake shekara ta hudu a fannin karatun likitan zata kafa tarihin zama likita ta farko makauniya kuma kurma.

Rahoto daga jaridar Daily Mail ya nuna yadda kurma kuma makauniyar dalibar ke amfani da na’urar jin magana don karfafa shigar sauti kunnenta.

Ta ce da yawa daga cikin marasa lafiya na karfafa mata guiwa, amma abokan karatunta na ganin kamar lalurarta zata hana ta cimma burinta.

KU KARANTA: An zo gurin: Zan cire duk wani jami'in kwastan da yake samun kudi fiye da albashin sa - Hameed Ali

Alexandra ta tuna yadda wani babban likita ya bata mata ranar farkonta da ta fara zuwa asibiti don sanin makamar aiki. Babban likitan ya bukaceta da ta koma gida saboda ba zata iya duba marasa lafiya ba.

“A ranar farkona a asibiti, wani babban likita ya sameni. Ya tambayeni idan ni mara lafiya ce ko zan bari nakasasshiyar likita ta duba ni. A take ya sanar dani cewa, marasa lafiya ba zasu bukaci aikina ba. Hakan kuwa yasa na koma gida rai a bace.”

Alexandra ta bayyana burinta na zama likitan kwakwalwa duk da akwai kalubale mai yawa da zata fuskanta. Tana fatan cikar burinta watarana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel