Binciken masana: Kwakwalwar mata ta fi ta maza aiki da kaifin tunani

Binciken masana: Kwakwalwar mata ta fi ta maza aiki da kaifin tunani

- Wasu kwararru a ilimin halayyar dan Adam na jami’ar California sun gano yadda kwakwalwar mace ta fi ta namiji aiki da kaifi

- Hakan kuwa ya bada hanyar gano manyan tambayoyin da masana kiwon lafiya ke yi game da cutar Alzheimer

- A wani binciken kuma, an gano cewa ‘ya’ya na gadon kaifin kwalkwalwa ne daga mahaifiyarsu ba daga mahaifi ba

Wasu kwararru a ilimin halayyar dan Adam na jami’ar California da ke kasar Amurka, sun gano yadda kwakwalwar mace ta fi ta namiji aiki da kaifi.

Masanan, wadanda suka gudanar da binciken a kan kwakwalwa dubu 46, sun bayyana cewa, a fannoni masu dumbin yawa, kwakwalwar mata ta zarce ta maza. Sun kara da cewa, sakamakon zai kawo wata sabuwar kofa ta fagen ilimin kiwon lafiya da kuma halayyar dan Adam.

Wannan binciken zai bada hanyar samo amsoshi masu yawa wadanda masana suka dade suna yi a kan cutar Alzheimer.

KU KARANTA: Bidiyo: Dan sanda ya fasawa soja kai cikin rashin sani yaje karbar cin hanci

Tun farko dai, an wallafa sakamakon binciken nan ne a mujallar kiwon lafiya ta 'Journal of Alzheimer’s Disease'.

A wani binciken kuma, an gano cewa, kaifin basira tare da ta kwakwalwa ana gadosu ne daga mahaifiya ba daga mahaifi ba.

A don haka ne masana suke bada shawara ga maza a kan su guji bin kyau wajen zaben ma ‘ya’yansu uwa. Zai fi kyau idan suka binciko mai kaifin kwakwalwa don suma ‘ya’yansu su gadota.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel