Rashin Imani: Miyagu sun shafe wasu iyalai gaba daya a jahar Benuwe
Wasu miyagu da ba’a san ko su wanene ba sun karar da wasu iyalai yan gida daya a jahar Benuwe, inda suka kashe maigidan, matarsa da wani ‘dansu guda daya, yayin da karamar diyarsu ta tsallake rijiya da baya.
Jarida Daily Trust ta ruwaito an tsinci gawar mamatan ne da sanyin safiyar Juma’a, 22 ga watan Nuwamba a gidansu dake unguwar North Bank, cikin garin Makurdin jahar Benuwe.
KU KARANTA: Magana daga bakin mai ita: Buhari yace baya sha’awar zarcewa a mulki karo na 3
Rahotanni sun bayyana sunayen mamatan kamar haka; Maigidan, Greg Indyor, matarsa, Linda da dansu Terkumawuese, inda ake zargin an kashesu ne yayin da suke cikin barci. Sai dai karamar diyarsu yar shekara 2 ta sha da kyar, inda aka tsinceta cikin mawuyacin hali.
A yanzu haka an garzaya da karamar yarinyar zuwa wani babban asibiti domin ceto rayuwarta. Sai shaidun gani da ido sun bayyana cewa da alama murde musu wuya aka yi, sai dai rundunar Yansandan jahar ta musanta hakan.
Kaakakin rundunar Yansandan jahar Benuwe, DSP Catherine Anene ta tabbatar da aukuwar lamarin yayin da take ganawa da manema labaru, inda tace babu wani tabbacin abin da ya kashe mamatan ko kuma yadda aka kashesu.
Anene ta kara da cewa a lokacin da Yansanda suka isa gidan mamatan da sanyin safiyar Juma’a basu tarar da wani ciwo ko rauni a jikinsu ba, balle kuma a yi zargin murde musu wuya aka yi, sa’annan tace yarinyar ta yi karama balle ta yi bayanin abin da ta sani.
Daga karshe dai kaakaki Catherine ta bayyana cewa bincike ne kadai zai tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar mamatan.
A wani labarin kuma, wani fitaccen malamin addinin kirista kuma fitaccen dan siyasa a jahar Edo, Fasto Aimola John ya yanke jiki ya fadi jim kadan bayan ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC tare da maigidansa Osagie Ize-Iyamu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng