Bidiyo: Dan sanda ya fasawa soja kai cikin rashin sani yaje karbar cin hanci

Bidiyo: Dan sanda ya fasawa soja kai cikin rashin sani yaje karbar cin hanci

- Wani jam’in dan sanda ya saka kanshi a cikin gagarumar rigima a bisa rashin sani

- Ya tsare katuwar mota da niyyar karbar cin hanci daga wajen direban motar, bai san cewa direban soja bane

- Tuni sojan ya sauko daga motar tare da cafke dan sandan, a take ya kira abokan aikinshi don su ladabtar da dan sandan

Wani jami’in dan sanda ya saka kanshi a cikin mummunan tashin hankali, bayan ya tare wata mota da niyyar ya karbi cin hanci daga wajen direban motar, ashe bai san cewa soja ne ba.

Kamar yadda rahoto ya nuna, jami’in dan sandan na tare da abokan aikinshi ne. Sojan bai yi kasa a guiwa ba wajen saukowa daga motar ya cafke dan sandan. Tuni sojan ya kira abokan aikinshi don taimaka mishi wajen ladabtar da jami'in dan sandan.

KU KARANTA: Bidiyo: Wani kifi mai fuskar Dan Adam ya hana mutane masu zuwa kogi sakat

A bidiyon da ke nuna yadda aka kwashe, daya daga cikin abokan aikin sojan, ya gaggauta isowa wajen. Ba yi wata-wata ba ya tube kayan aikinshi don fara abinda ya dace.

Duk da bamu tabbatar da inda lamarin ya faru ba, ga dai bidiyon yadda abun ya kasance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel