Bidiyo: Wani kifi mai fuskar Dan Adam ya hana mutane masu zuwa kogi sakat

Bidiyo: Wani kifi mai fuskar Dan Adam ya hana mutane masu zuwa kogi sakat

- Wani kifi mai fuskar mutum ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta na zamani

- Kifin wanda yake da fuskar mutum dai an gano shi ne a wani Kogi da ke kasar China

- Mutane da yawa sun firgita da ganin kifin saboda tsananin kamar da fuskarshi tayi da ta mutane

Wani kifi mai fuskar mutum ya tada hankulan mutane kuma ya zama abin magana a kafafen sadarwa. An wallafa bidiyon kifin ne wanda ke yawo a cikin ruwa a hankali kamar mutum, saboda yanayin fuskarshi.

Cikin kwanakin nan ne aka wallafa hoton wani kare mai suna Nori da ke da fuskar mutum. Wasu sun yarda kare ne amma wasu sun karyata hakan. Ana zargin ko an hada jikin karen ne da fuskar mutum.

Kwatsam kuma sai ga kifi mai fuskar mutum da ke rayuwar a cikin ruwa. Wannan kifin dai an gano shi ne a wani kogi da ke kasar China. Fuskarshi abin al’ajabi ce sakamakon kamar da ya yi da mutane.

KU KARANTA: Innalillahi: Daga zuwa gidan biki yaro ya tsunduma cikin tukunyar girkin abincin biki

Wani bako mai yawon shakatawa ne da ya ziyarci Kunming a kudancin China ya dauki bidiyon kifin. Hakan kuwa ya dinga firgita mutane tare da basu tsoro saboda yadda kifin ke ninkaya a cikin kogin.

Bakon ya wallafa bidiyon ne a shafinsa na sada zumuntar zamani na Weibo da kasar China ke amfani da shi. A bidiyon an ga kifin na tasowa saman ruwan dauke da fuskar mutum.

A fuskar kifin kuwa, akwai shaidar ido da wata alama kamar hanci tare da siffar bakin mutum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel