Labari mai dadi: An bude jami'ar kudi ta farko a jihar Jigawa

Labari mai dadi: An bude jami'ar kudi ta farko a jihar Jigawa

- Hukumar kula da jami’o’i ta kasa, tace jami’ar kudi ta farko a jihar Jigawa ta kusa samun lasisi

- Hukumar ta sanar da hakan ne a ziyarar duba ginin jami’ar na dindindin da ta yi

- Wannan ne karo na biyu da hukumar ta kai ziyara ga ginin jami’ar don ganin yadda aka tsaidashi

Hukumar kula da jami’o’i na kasa (NUC) ta ce, jami’ar farko ta kudi da ake yunkurin budewa a jihar Jigawa ta cika sharudda 10 cikin 14 da hukumar ta shimfida mata.

Jami’ar Khadija Majiya ta tsallake matakai 10 cikin 14 da zata cika kafin a bata amincewar karshe tare da lasisin fara karatu.

Mukaddashin daraktan NUC a kan kafa jami’o’in kudin, Farfesa Aminu Abba, ya sanar da hakan yayin dubiyar filin ginin jami’ar na dindindin.

Ya nuna gamsuwarshi a kan cigaban da ya gani a filin ginin sabuwar jami’ar.

Kamar yadda Farfesa Abba ya ce, wannan ne karo na biyu da hukumar ta kai ziyara filin da ake gina jami’ar. Ya kara da cewa, hukumar ba zata sassauta dokokinta na gwamnatin tarayya ba a kan ilimin jami’o’in kudi.

KU KARANTA: Daga tambaya sai cibi ya zama kari: Matashi ya kashe wata mata mai ciki saboda kawai ta tambayeshi ranar da zai yi aure

Ya ce, amfanin ziyarar, shine sauke faralin NUC din tare da ganin yadda ginin jami’ar ya tsaru don amincewarsu.

A yayin jawabin shugaban tsari da tabbartarwa na jami’ar Khadija Majiya, Farfesa Sagir Adamu Abba, ya jinjinawa kungiyar a kan kokarinta na kawo ziyarar a lokacin da ya dace, duk da nauyin da ke kanta.

Ya cigaba da jinjinawa wanda ya kirkiro jami’ar, Adam Musa Majiya, wanda ya kwatanta da dan kasa nagari, mai aiki tukuru kuma ba don kanshi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel