Kulawa da walwalar ma’aikata shine babban abin dake gabana a yanzu – Buhari

Kulawa da walwalar ma’aikata shine babban abin dake gabana a yanzu – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kulawa da walwalar ma’aikata tare da biyan bukatun ma’aikatan Najeriya shi ne babbar abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai a yanzu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito shugaban ya bayyana haka ne yayin taron kungiyar kwadago ta duniya, ITU karo na hudu daya gudana a babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Babban magana: Dino Melaye ya mika ma INEC bidiyo 21 dake nuna yadda APC ta yi magudi

A jawabinsa, Buhari ya shaida ma mahalarta taron cewa gwamnatinsa na da kyakkyawar alaka da ma’aikata, kuma ya fahimci matsalolinsu haka zalika yana sanya lura da nuna damuwa wajen warware dukkanin matsalolin nasu.

Babban sakataren ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Olusegun Olakunle ne ya wakilci shugaba Buhari a yayin taron, kuma yace a lokacin da suka dare madafan iko a shekarar 2015 sun tarar da bashin albashi da alawus alawus da ma’aikata dayn fansho suke bin gwamnati.

Amma suka jajirce wajen tabbatar da sun sauke wannan nauyi dake wuyan gwamnati ta hanyar biyan bashin albashin ma’aikata, alawus dinsu da kuma kudaden yan fansho, haka zalika sun taimaka ma jahohin Najeriya wajen sauke wannan nauyi.

Da wannan ne shugaban kasa ya yi kira ga shuwagabannin kungiyoyin kwadago dasu dage wajen kare muradun jama’a ta hanyar nuna kwazo wajen gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da suna aikinsu yadda ya kamata.

“Baya ga biyan basussukan albashi a matakin jahohi, kananan hukumomi da na tarayya, mun kara ma hukumar biyan yan fansho ta wucin gadi, PTAD karfi domin ta cigaba da gudanar da aikinta cikin sauki, bugu da kari mun gudanar da garambawul ga tsarin fanshon Sojoji.

“Watanni kadan da suka gabata muka amince da sakan tsofaffin ma’aikatan tsohuwar kamfanin sufurin jiragen sama ta Najeriya, Nigerian Airways hakkokinsu, wanda suke bin bashin kusan shekaru 20. Don haka batun walwalar ma’aikata na daga cikin muhimman lamurran da muka sanya a gabanmu.” Inji shi.

Daga karshe shugaban kasa ya bayyana cewa sun kara karancin albashin ma’aikaci daga N18,000 zuwa N30,000 sakamakon sanin muhimmancin ma’aikaci a tsarin gwmanati, domin kuwa idan ma’aikaci ya gaza wajen gudanar da aikinsa, gwamnati ba za ta taba samun nasara ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel