Wata sabuwa: Za a rushe gine-gine 140 a tsakiyar birnin tarayya

Wata sabuwa: Za a rushe gine-gine 140 a tsakiyar birnin tarayya

- Hukumar da ke kula da tsarin gine-ginen tsakiyar birnin Abuja, ta yi wa gine-gine 140 shaida

- Shugaban bangaren tsari da habaka na yankin, ya ce gine-ginen an yi su ne ba bisa ka'ida ba

- Tuni dai suka sanar da wadanda abun ya shafa tare da basu umarnin tattara komatsansu

Hukumar da ke kula da tsarin gine-ginen tsakiyar birnin Abuja ta yi wa gine-gine 140 shaida don rushewa a yankin Guzape na babban birnin tarayya a Abuja.

A yayin tattaunawa da manema labarai bayan da ya kammala duba gine-ginen, shugaban bangaren tsari da habaka na yankin, Thompson Hope, yace gine-ginen da rusau din ya shafa sune a yankin Kpaduma II da Kuruduma II na Guzape.

DUBA WANNAN: Hukumar Kwastam ta nada sabbin shugabanni, ta yi wa jami'ai 2,408 karin girma (Jerin sunaye)

Ya kara da cewa, gine-ginen da abun ya shafa duk an yi musu shaida kuma an sanar da wadanda ke ciki da su hanzarta tattara komatsansu kafin ranar da za a fara rushe-rushen.

Ya ce, bangaren cigaba da habakar na tarayyar ya dade yana wayar wa da mutanen yankin kai, amma sun ki bin asalin tsarin da wurin ya ginu a kai.

Hope ya ce, ba su kadai ba, akwai wasu wurare na yankin da rusau din zai ritsa dasu kuma duk sunyi shaida. Sun kuma sanar da mutanen yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel