Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

- Sajad Gharibi wani gabjejen mutum ne dan asalin kasar Iran

- Zai fara wasan damben kokawa ne a shekara mai zuwa sakamakon sa hannun kwangilarshi da kungiyar damben kokawa ta BKFC

- A shekarar 2016, Gharibi ya yi tayin shiga rundunar sojin Iran don yakar ‘yan ta’addar ISIS

Sajad Gharibi, wani gabjejen mutum ne dan asalin kasar Iran da ake kira da ‘Iranian Hulk’ ko kuma ‘Persian Hecules saboda girman jikinshi. Sunanshi ya cika kanun labarai bayan da yasa hannu a sabuwar kwangila da wata kungiya ta damben kokawa mai suna Bare Knuckle Fighting Championship, inda zai fara wasan dambe a matsayin kwararren dan damben kokawa.

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS
Source: Facebook

A shekarar 2016, Gharibi ya cika kanun labarai tare da samun mabiya kusan 500,000 sakamakon tayin shiga mayakan kasar Iran da yayi don yakar ‘yan ta’addar ISIS da suka gallabesu.

Amma kuma nauyinshi na kilogiram 175 ya ba mutane da yawa mamakin yadda ya yanke shawarar fadawa harkar damben kokawa.

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS
Source: Facebook

KU KARANTA: Allahu Akbar: Dan wasan kasar Amurka Van Damme ya shawarci mutane suyi koyi da abinda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar

Shugaban kungiyar ta damben kokawa ta BKFC, David Feldman, ya ce sabuwar kwangilar da suka fara zantawa da Gharibi zata kammalu ne a ranar Litinin.

“Zai shiga cikin ‘yan wasan kokawar BKFC a farkon shekarar 2020. Zamu yi wani wasa mai suna ‘Amurka da Iran: Yakin duniya na uku’. A gaskiya shi ne mutum mafi girma da muka taba sa hannun kwangila da shi. Amma muna da tabbacin ya samu gida. Muna tsammanin nasarori masu yawa daga ‘Iranian Hulk’.”

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS
Source: Facebook

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS

Hotuna: Sajad Gharibi kenan gabjejen katon da ya sha alwashin ganin bayan kungiyar ISIS
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel