Tirkashi: Babu Coach din da ya isa ya hanani bautar ubangijina a duniyar nan - Ahmed Musa

Tirkashi: Babu Coach din da ya isa ya hanani bautar ubangijina a duniyar nan - Ahmed Musa

- Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Ahmed Musa, ya mika godiyarshi ga shuwagabannin ‘yan wasa

- Ya bayyana yadda suke tausaya mishi yayin da ake wasa ko horarwa kuma yana azumi

- Musa ya yi azumi a lokutan wasan gasar kofin duniya a 2014 da 2018 kuma duk da haka ya saka kwallo a raga

Kyaftin din kungiyar kwallon kafan Najeriya, Ahmed Musa, ya nuna godiyarshi ga shuwagabannin ‘yan wasa a kan yadda suke mishi in yana azumi. Amma yace, babu abinda zai hanashi azumin shi tunda ibada ne, kuma baya hana shi harkokinshi.

“Tun ina karamin yaro nake azumi. Bana tunanin zan iya dena azumin, saboda na zama kwararren dan wasan kwallon kafa. Na yi wasanni da yawa tare da horarwa kuma duk a cikin watan Ramadan, kuma babu abinda hakan ya canza.”

“A matsayin dan wasan kwallon kafa kuma musulmi, ba ni da wani dalili na kin yin azumin watan Ramadan. An amince mana da kada mu yi azumi ne idan muna kan hanyar doguwar tafiya, a kalla wacce zata dau sa’o’I hudu zuwa biyar.”

“Da yawan shuwagabannin ‘yan wasa wadanda ba musulmai ba kan tausaya min. Suna mamakin yadda nake iya wasa bayan ina azumi. Amma addinina ne kuma babu abinda zai hanani yin shi. Dole ne in mutunta addinina,” Musa ya sanar da Opera News.

Musa ya yi azumi a lokacin gasar kofin duniya na shekarar 2014 da 2018, kuma duk ya yi nasarar wurga kwallo cikin raga a dukkan wasannin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel