Ba wani abu bane dan jaruma tayi aure an saketa ta sake dawowa harkar fim - In ji Ummi Duniyar Nan
- Daya daga cikin jarumai mata masu tasowa, Ummi El-Abdul ta bayyana yadda sana’ar fim ta zamar ma wasu sana’a abar dogaro
- Jarumar mai tasowa tace, harkar fim bata hana yin aure musamman ga mata masu yin harkar kuma da niyyar auren
- Ta ce ba aibu bane don mace ta yi aure ta fito, ta dawo harkar fim din
Daya daga cikin jarumai mata masu tasowa a masana’antar Kannywood, Ummi El-Abdul wadda aka fi sani da Ummi duniyar nan ta bayyana harkar fim a matsayin wata harka ta sana’a da neman rufin asiri ga masu yinta. Don haka ba wata harka ba ce da take hana yin aure musamman ga mata masu yin harkar.
Jarumar ta bayyana haka ne ga wakilin jaridar dimokaradiyya a lokacin da suke tattaunawa dangane da kallon da ake musu. Kuma na cewa, duk wacce ta shiga harkar fim, ta kan jingine maganar aure ne ta mike kafa ta dinga yadda ta ke so.
Jarumar ta fara bada amsa da cewa: “Kawai ina ganin fassara ce irin ta mutane wadanda basu da masaniya a kan al’amarin. Amma komai dadin da kikeji, zaki so hankalin iyayenki ya kwanta kema ki yi auren. Sai dai idan dama can mace bata da niyya.”
KU KARANTA: Tonan silili: Fasto ya tilasta amarya ta cire kayan amarci saboda an taba kwanciya da ita
An tambayeta ra’ayinta akan yadda ‘yan fim ke yin aure, su fito kuma su koma harkar fim. Sai tace, “Ai abinda mutane basu sani ba shine, koda yarinya ta yi aure, saboda rashin fahimtar da mutane ba sa yi mana, sai ki ga iyaye da dangin miji sun sanya ta gaba sai sun ga bayan auren. Toh ni a ganina, don an saki ‘yar fim ta dawo fim, ba wani abu bane, domin wata idan ba a saka ta ba, sai ta kama wata hanya daban.”
Daga karshe, ummi ta yi kira ga jama’a da su dinga musu uziri domin su ma ‘yan fim mutane ne kamar kowa, zasu iya yin daidai kuma zasu iya yin kuskure
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng