Gaskiya da rikon amana: Buhari ya karrama tsohuwar ma'aikaciyar MMIA

Gaskiya da rikon amana: Buhari ya karrama tsohuwar ma'aikaciyar MMIA

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC ta karrama wata tsohuwar ma'aikataciyar filin tashi da saukan jirage na Murtala Mohammed (MMIA) dake Legas, Misis Josephine Ugwu wacce a lokuta daban-daban ta tsinci miliyoyin naira da matafiya suka manta da shi a ban daki amma ta mika wa jami'an tsaro don a bawa masu kudin.

A yau ne Talata 11 ga watan Nuwamba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata lambar yabo ta gaskiya da rikon amana na hukumar ICPC don irin halayenta na gaskiya.

Kazalika, shugaban kasar ya mika lambar yabbon ta gaskiya da rikon amana ga Bashir Abubakar, mataimakin kwantrola janar na kwastam da ya ki karbar rashawa ta $412,000 da kan ko wane kwantena daya ta kwayar tramadol da wasu masu safarar kwaya suka nemi biyansa yayin da suke yunkurin shigo da kwantena 40 na kwayar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Hadimin Atiku na kut-da-kut ya rasu

A dai wurin taron, Shugaba Muhammadu Buhari, ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi gaggawar amince wa da kudirin hukunta masu aikata laifuka na musamman.

A jawabin da ya yi wurin taron kasa na kan 'Hanyoyin rage rashawa a aikin gwamnati da Hukumar Yaki da Rashawa (ICPC) tare da hadin gwiwar ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka shirya, shugaban kasar ya bukaci bangaren shari'a su amince da kirkirar kotunnan laifuka na musamman.

Ya ce, "Yaki da rashawa ba ya rataya kawai a wuyan gwamnati bane da hukumomin yaki da rashawa. Dukkan bangarorin gwamnati sai sun hada karfi wuri guda don kirkirar hanyoyin magance rashawar.

"Ina gayyatar bangaren shari'a da na majalisa su rungumi tare da goyon bayan kirkirar kotunnan sauraron kararraki kan laifuka na musamman da 'yan Najeriya ke neman a kafa domin kulawa da laifukan rashawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel