Jerin kasashen da suka fi ko ina hadari a duniya a shekarar 2020

Jerin kasashen da suka fi ko ina hadari a duniya a shekarar 2020

- Sabuwar taswirar tafiye-tafiye ta shekarar 2020 da ta fito, an bayyana wurare masu matukar hatsari a duniya

- Kwararrun masana a fannin hatsarin kasashe na duniya sun fitar da taswirar a kan kiwon lafiya, tsaro da ingantattun tituna

- A fannin lafiya da tsaro, anyi kididdigar ne a cikin mutane biyar, inda na lafiyar tituna aka yi kididdigar a kan yawan mutanen da ke mutuwa duk cikin mutane 100,000

A sabuwar taswirar tafiye-tafiye ta duniya ta shekarar 2020 da ta fito, an bayyana kasashe masu matukar hatsarin gaske a duniya.

Kasashen Libya, Somalia, Sudan ta kudu da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun bayyana a matsayin kasashe mafiya hatsari a duniya kamar yadda taswirar ta bayyana.

Kwararrun masana a fannin kasashe masu hatsari na duniya sun fitar da taswirar ne a kan abubuwa uku, wadanda suka hada da: kiwon lafiya, tsaro da lafiyar tituna.

A cikin kididdigar da masanan suka yi, kasashen Iceland, Norway, Finland, Denmark, Switzerland, Luxemborg, Slovenia, Andorra da Svalbard ne suka kasance kan gaba a fannin kiwon lafiya ingantacciya, tsaro da lafiyar tituna.

KU KARANTA: Bidiyon yadda Sadiya Haruna da Isah A Isah suke kokarin sumbatar junansu

Kasashen da ke da matukar hatsari ta fannin tsaro sun hada da Mali a arewa maso yammacin nahiyar Afirka, Syria, Yemen da Afghanistan.

Kasashen Venezuela, Haiti, Koriya ta arewa, Syria, Iraqi, Afghanistan, Yemen, Eritrea, Burkina Faso, Niger, Guinea, Sierra Leone, Liberia, Guinea-Bissau da Burundi ne aka gano suna da manyan hadurra ta fannin kiwon lafiya.

Kasashe masu matukar hatsari ta fuskar tsaro sun hada da: Libya, Somalia, South Sudan, Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, Mali, Syria, Iraqi, Yemen da Afghanistan. Kasashen da basu da hatsari ta fuskar tsaro a duniya sun hada da: Iceland, Norway, Finland, Denmark, Switzerland, Luxemborg, Slovenia, Andorra, Svalbard da kasar Greenland.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel