Yansanda sun tabbatar da kisan dan uwan Sanata Ibrahim Mantu

Yansanda sun tabbatar da kisan dan uwan Sanata Ibrahim Mantu

Rundunar Yansandan jahar Filato ta tabbatar da kisan wani dan uwan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, Hashimu Mantu, kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana.

Kaakakin Yansandan jahar, DSP Terna Tyopev ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, inda yace an gano gawar Hashimu ne a kauyen Chanso dake garin Gindiri, karamar hukumar Mangu.

KU KARANTA: Kwararowar hamada: Gwamna ya sanya kyautar naira dubu 100 ga duk mutumin daya dasa bishiya

“A ranar 16 ga watan Nuwambar 2019 da misalin karfe 6:30 na safe muka samu rahoton wani gawa a wani daji dake kusa da kauyen Chanso a karamar hukumar Mangu. Jim kadan Yansanda suka isa dajin, inda muka gano Hashimu Mantu ne dan shekara 42.

“Koda muka garzaya da shi Asibitin koyarwa na jami’ar Jos, inda likitan dake aiki a ranar ya tabbatar mana da cewa ya mutu.” Inji Tyopev.

Kaakakin yace sun gano wayar salulan mamacin, da wani sanda a gefensa, daga bisani Yansanda sun mika gawar mamacin ga iyalansa domin su yi masa jana’iza bisa koyarwar addinin Musulunci.

Daga karshe rundunar tace tana cigaba da kokarin gano duk masu hannu cikin kisan Mantu, domin tabbatar da sun fuskanci hukunci yadda ya kamata, don haka take kira ga jama’a da cewa duk wanda ya san wani abu game da lamarin ya taimaka mata da bayanai.

A wani labari kuma, Rundunar Yansandan jahar Imo ta sanar da kama wata mata mai suna Ukamaka Ezike wanda ake zarginta da kashe ‘ya’yanata mata guda biyu masu kananan shekaru.

Mijin matar, kuma mahaifin yaran, mai suna Christian Ezike mazaunin unguwar Awo Idemili dake cikin karamar hukumar Orsu na jahar Imo ne ya kai kara ga Yansanda.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel