Yadda wani furodusa ya nemi yayi zina dani na tsawon sati daya kafin ya sanya ni a wani sabon fim - In ji wata fitacciyar jaruma

Yadda wani furodusa ya nemi yayi zina dani na tsawon sati daya kafin ya sanya ni a wani sabon fim - In ji wata fitacciyar jaruma

- Wata fitacciyar jarumar masana’antar Nollywood kuma mawakiya ta bayyana karonta da furodusoshi masu lalata da jarumai

- Ta bayyana cewa furodusan ya nemi kwanciya da ita na mako daya kafin ya sanyata a shirin fim dinshi da suka gama ciniki

- Ta bayyana yadda ta fuskanci kalubale mai tarin yawa tare da barazanar ganin kamar burinta ba zai cika ba

Fitacciyar jaruma, mawakiya sannan kuma masaniya a fannin gyaran fata, Chieneye Esther Anakulu Nze wacce aka fi sani da Chesan Nze, bata cikin mutane masu boye harkar rayuwarsu, domin kuwa ta kan bayyana abinda ta ke ciki kuma yadda yake.

Cikin kwanakin nan ne ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram a kan furodusoshi masu bukatar kwanciya da ‘yan wasa kafin su saka su a fim dinsu. A tambayar da jaridar Gistmania ta yi mata a kan dalilin rubutun, ga abinda jarumar ta ce:

“Babu dadewa na koma Legas don cika burina na zama ‘yar wasan kwaikwayo. Tun daga nan kuwa, furodusoshi da yawa sun dinga nemana don fitowa a shirinsu. Bayan amincewa kuwa, sai a kirani taro wanda daga shi ake fara gayyatar mutum dakin otal din furodusa. Rashin amincewa ke sa a maye gurbinka da wata a take a wajen.”

“Wannan rubutun da na wallafa kuwa nayi ne saboda wani furodusa. Ya bukaci inyi aiki dashi har mun kammala ciniki. Kwatsam sai ya bukaci sai ya kwanta da ni na sati daya kafin mu fara aiki. Na firgita matuka kuma na sanar dashi, babu yadda za a yi in kwanta dashi ko wani saboda zan yi fim dinshi. A take ya katse wayar. Na yi kukan bakin ciki saboda a ganina ya tozarta ni a matsayina na mace, haka ya sanya nayi wannan rubutu a shafina na Instagram.”

KU KARANTA: Bayyanar Maryam Yahaya a harkar fim ne ya budewa kananan yara kofar shiga harkar - Tashar Tsakar Gida

Jaridar ta kara da tambayarta cewa, mutane da yawa na tsoron bude baki su yi magana akan irin wannan lamarin, shin baki samu wata barazana ba bayan rubutun naki? Ga amsar da ta bada:

”Gaskiya an yi min barazana. Wasu mutanen ce min suka yi, ina ganganci da aikina tare da cikar burina saboda na fadi gaskiya. Wasu mutanen kuwa karfin guiwa suka kara min a kan cewa kada in bada kai bori ya hau. Sun kara da hadani da furodusoshi nagari. Kafin in fara wasan kwaikwayo, na yi alkawarin yaki da duk wata badala da ke masana’antar. Ina son suna mai kyau kuma ina son zama wacce mutane zasu kalla a matsayin madubin dubawa ma'ana abar koyi a harkar fim.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng