Adam Zango ya ciri tuta a matsayin jarumin da ya fi taimaka ma talakawa
Gidauniyar Hope Foundation da kamfanin Arewa Films production sun karrama shahararren jarumin fina finan Kannywood, Adam A Zango da lambar yabo ta ‘Philantrophist of the year’, ma’ana gwarzon da ya fi tallafa ma gajiyayyu da talakawa a shekarar 2019.
Haka zalika kungiyoyin sun karrama Adam Zango a matsayin gwarzon shekara da yan kallo suka fi kauna, watau ‘Viwers choice of the year.’ Kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito,
KU KARANTA: Kaico! Wata mahafiya ta kashe ‘ya’yanta mata guda 2 a jahar Imo
Kungiyoyin sun karrama A Zango ne biyo bayan tallafin daya baiwa wasu dalibai marayu da gajiyayyu dake makarantar Professors group of schools dake Zaria, ta hanyar biya musu kudin makaranta gaba dayansu.
Idan za’a tuna Adam Zango ya dauki nauyin dalibai 101, inda ya biya musu kimanin kudi naira miliyan 46.7 na tsawon shekaru uku a makarantar.
A wani labari kuma, Adam A. Zango ya bayyana cewa mutane hudu ne suka Musulunta a sanadiyar fim dinsa na ahlul Kitabi, sa’annan ya bayyana cewa tunda aka kafa masana’antar Kannywood babu wani jarumi da ya yi fina-finan fadakarwa tare da kira zuwa ga addinin Musulunci kamar shi.
Jarumin ya bayyana cewa duk da wannan kokari da yayi babu wani malami da ya taba kiransa ya bashi lambar yabo koda na katako ne, sai dai zagi da hantara.
“Mutane 4 ne suka musulunta sanadin Film dina na ahlul kitabi. Kazalika tunda aka kirkiro Kannywood babu wani jarumi dayayi fina finan Fadakarwa tare da kira akan tafarkin Addinin Islama kamarni Adam A Zango.
“Amma duk da wannan kokari da muke yi, babu wani Malamin addini da ya kiramu ya bamu koda lambar yabon katako! Sai zagi da neman Kuskurar da kokarin da muke yi.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng