Da duminsa: INEC ta soke zabe a wani gari a Bayelsa

Da duminsa: INEC ta soke zabe a wani gari a Bayelsa

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta soke zabe a Ologi (ward 3) da ke karamar hukumar Ogbi na jihar Bayelsa sakamakon barkewar rikici a yankin da ya hada da sace wani jami'in zabe.

Jami'in INEC, kuma kwamishinan zabe na karamar hukumar Ogbia, Ukuachukwu Orji ya ce al'ummar garin na Ologi sun hana zabe karfe da yaji kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce, "A lokacin da mutanen mu (ma'aikatan zabe) ke shiga garin bayan sun tsallaka rafi, sun kama su sannan suka kwace kayayyakin zaben suka kona.

"Sun kori wasu daga cikin ma'aikatan mu, sun kuma rike wasu amma daga bisani sojoji sun ceto su."

Mr Orji wanda a baya shine jami'in zabe na jihar Anambra, ya yi magana a Otuoke (ward 13 na karamar hukumar Ogbia) inda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da iyalansa suka jefa kuri'arsu.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan daba sun sace akwatunan zabe a rumfar zaben Dino Melaye

Ya ce rikicin da al'ummar garin suka tayar ne ya yi sanadiyar soke zaben don gudun tabarbarewar tsaro.

Ya kuma bayyana gamsuwarsa kan yadda zaben ke tafi lami lafiya a wasu sassa na jihar baya ga karamar hukumar Ologi.

Ana gudanar da zaben gwamnan ne a dukkan kananan hukumomi takwas da ke jihar ta Bayelsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164