Tirkashi: Ko uwa ta ba ta isa ta raba ni da Zahraddeen Sani ba - Adama Muhammad

Tirkashi: Ko uwa ta ba ta isa ta raba ni da Zahraddeen Sani ba - Adama Muhammad

-Jaruman fina-finan Hausa kan samu masoya masu tarin yawa wadanda suke sha’awar fina-finansu

- Farin jinin nan kuwa ne ya jawo wata mata mai suna Adama Muhammad ga Zahradeen Sani

- Bayan kwanaki hudu kacal kuwa da haduwa suka danganta da kotu a kan zargin saba alkwarin aure da ta ke mishi

A bangaren jarumin, Allah ya hada shi da wata mata mai son shi wacce bayan sun fara mu’amala da kwanaki hudu gayyar ta watse. Ba a nan abun ya tsaya ba yanzu haka an danganta da kotu.

Matar mai suna Adama Muhammad, ta sha alwashin sai ta auri jarumin ko ta wanne hali ne kuwa.

Matar ta maka jarumin a kotu a kan zarginshi da take da yi mata alkawarin aure kuma ya saba.

A zaman kotun da aka yi, wanda Adama ce ta kai jarumin kara kotun musulunci da ke Titin Rock a Tudun Nufawa, Kaduna, ta zargi Zahradeen Sani da abokansa; Ishaq Sani da Malam Turaki, a kan saba alkawarin aure.

Jarumin bai samu halartar kotun ba amma lauyanshi ya sanar da uzirinshi. Ya kara da sanar da alkali cewa, jarumin ya shigar da kara kafin nan kuma sun buga hujjojinsu a wasu jaridu. Alkalin ya bukaci da a kawo su a zama na gaba.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne aka shiga kotun Majistare da ke NDA, Badarawa Kaduna don sauraron karar da Zahradeen ya shigar a kan tuhumar Adama da bata mishi suna.

Dukkansu kuwa sun halarci kotun amma daga bisani an yanke hukuncin su je gida su yi sasanci.

Bayan fitowa daga kotun, an ji Adama na cewa, “wallahi ko uwa ta ba ta isa ta sa a yi wannan sasancin ba!”

An so jin ta bakinta amma sai taki Magana.

Da wakilin Mujallar Fim ya tuntubi jarumin don jin abinda ya hadashi da matar, yace “Ta bayyana ne a matsayin mai son fina-finai na amma ta yi ta kokarin shiga jikina. Bayan kwanaki hudu da haduwarmu na gane tafiyarmu ba zata zama daya ba. Ta zagi wata budurwa mai sha’awar fina-finai na bayan da ta ganmu tare,”

“Tun bayan haduwarmu ta ke ce min tare da abokai na tana so mu yi soyayya har mu yi aure. Tace ita P.A din shugaban majalisar dattawa ce, budurwar El-Rufai ce, zata samo mana kwangila, za ta sa a bamu man fetur, ta san Ibrahim Badamasi Babangida don saurayinta ne,”

Jarumin y ace, bai taba cin komai na Adam aba amma ta ke neman bata msihi suna. Su kuwa abokanshi da ta hada dasu, saboda sun ki sasanta su ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel