Allahu Akbar: Wata mata ta shafe shekara 32 tana saka Al-Qur'ani mai girma da zare da allura tun daga Bakara har Nasi

Allahu Akbar: Wata mata ta shafe shekara 32 tana saka Al-Qur'ani mai girma da zare da allura tun daga Bakara har Nasi

- Wata mata mai suna Naseem Akhtar ta samu kammala dinka Al-Qur’ani mai girma

- Ta kafa wannan tarihin ne a cikin shekaru 32, aikin da ta fara tun tana matashiyar budurwa

- Naseem ta bayyana cewa, babu abinda ya taba bata gamsuwa da farin ciki kamar wannan aikin da ta yi

Mace ta farko a duniya da ta fara dinka Al-Qur’ani da hannu, mace ce ‘yar kasar Pakisatn mai suna Naseem Akhtar. Ta samu wannan baiwa ta zama mutum ta farko a duniya da ta dinka Al-Qur'ani. Wannan kirkirar na bayyana kokari, juriya, jajircewa da soyayyarta ga Musulunci da Al-Qur’ani mai girma.

“Na fara dinkin Al-Qur’anin ne ba tare da na yi tunanin lokacin da zan dauka ba. Ina godiya ga Ubangiji da ya bani ikon kammala wannan aikin. Ina farin ciki da hakan. Ban taba farin ciki a duk rayuwata ba kamar na yau.”

Naseem Akhtar ta dau shekaru 32 tana wannan aikin kafin ta kammala. Ta fara aikin ne lokacin da take matashiyar budurwa. Duk da bata san aikin zai dauki dogon lokaci ba kafin ta kammala. Ta bayyana cewa, babu dana sani a jajircewar da ta yi saboda Allah da Al-Qur'ani.

Kamar yadda Naseem ta ce, babu wani abu a lokacin rayuwarta da ya bata gamsuwa da farin ciki kamar yadda wannan ya bata. Tana kara godiya ga Allah.

KU KARANTA: Sal Lavallo: Yana da shekara 27 ya ziyarci kowacce kasa a duniya yana neman addinin gaskiya, Allah da ikon sa yanzu dai ya Musulunta

Nauyin Qur’anin da Naseem ta dinka zai kai kilogram 60 kuma an yi shi ne daga auduga. Yana da ado mai kalar zinari. Murfin shi yana da shingen siliki inda kowacce surah ke da salo iri daya. A farkon kowacce surah, akwai murfinta. Ta dinke duk surorin da zare mai kalar kore. Ta yi duk wadannan aiyukan da hannunta ne ba tare da amfani da wata na’ura ba. Bata kuma bukaci tallafin kowa ba yayin aikin.

Naseem Akhtar a halin yanzu tana zama ne a Gujrat, Pakistan. Lokacin da jami’an kasar Saudi suka ji labarin wannan aikin nata, sai suka gayyaceta kasar tasu ta Saudi Arabia.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel