Ashshsa! Jirgin rundunar dakarun Sojan saman Najeriya fado a jahar Enugu

Ashshsa! Jirgin rundunar dakarun Sojan saman Najeriya fado a jahar Enugu

Wani jirgin sama mai tashin angulu mallakain rundunar Sojan saman Najeriya ya fado kasa tim a yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa daga atisaye a jahar Enugu, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shi dai wannan jirgi daya gamu da hatsarin da shi ne rundunar take amfani wajen horas da dakarunta yadda zasu iya sarrafa jirgin yaki, da kuma koyon dabarun yakin sama.

KU KARANTA: Inganta tsaro: Babban sufetan Yansanda ya nada sabbin kwamishinoni a jahohi 7

Hukumar Sojan sama da kanta ta tabbatar da wannan lamari ta shafinta na kafar sadarwar zamani na Twitter, inda tace lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba bayan an dawo da shi daga atisaye.

Sai dai duk da rundunar ta tabbatar da cewa babu wanda ya samu rauni ko ya mutu a sakamakon hadarin, amma dai rundunar bata bada cikakken bayani game da musabbabin aukuwar hatsarin ba.

Kaakakin rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ya bayyana cewa: “Jirgin Saman rundunar Sojan sama ya gamu da hatsari yayin da yake sauka a jahar Enugu. Jirgin ya fado ne bayan ya dawo daga atisaye, amma babu wani Soja dake cikin jirgin daya jikkata.

“Tuni babban hafsan sojan sama, AM Sadique ya bada umarnin a kafa kwamitin bincike da zata gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da musabbabin aukuwar hatsarin. Da wannan ne rundunar sojan sama ke cigaba da neman goyon bayan jama’a a kokarin da take yi na tabbatar da tsaro a Najeriya gaba daya.” Inji shi.

A wani labarin kuma, babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu ya aika da sabbin kwamishinonin Yansanda zuwa wasu jahohin Najeriya guda 7 domin samar da ingantaccen tsaro a cikin jahohin da kewayensu.

Ga sunayen sunayen sabbin kwamishinonin da jahohinsu kamar haka; Habu Sani Ahmadu jahar Kano, Lawal Jimeta jahar Edo, Phillip Sule Maku jahar Bauchi, Nkereuwem A Akpan jahar Cross Rivers, Kenneth Ebrimson jahar Akwa Ibom, Odumusu Olusegun jahar Legas da Imohimi Edgal jahar Ogun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng