Pantami ya yi umurnin dakatar da sakon voicemail kai tsaye a layukan waya

Pantami ya yi umurnin dakatar da sakon voicemail kai tsaye a layukan waya

Ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya ba kamfanonin layukan waya umurnin datse sakon voice mail kai tsaye a layukan mutane.

A wata sanarwa daga kakakin ministan, Uwa Suleiman ta bayyana cewa ministan ya gano cewa lamarin ya fara zama ruwan dare alhalin hakan ya zamo bakon abu a Najeriya.

Ya kara da cewa mutanen da ke zauna a karkara ba sa fahimtar yaren da kamfanonin ke amfani da shi a sakonnin sannan cewa kamata ya yi mutum ya zabi abunda ya ke so da kansa amma ba wai a canja masa akalar kiran nasa ba ba tare da son ransa ba.

Sanarwar ya ce: "Hakki ne da ya rataya a wuyarmu kare hakkin masu amfani da layuka a Najeriya yayin da kuma muke samar da yanayin kasuwanci ga kamfanonin layukan bisa tsarin kasuwanci na duniya.

"Hakan ne dalili da ya sa Dr. Pantami ya umarci hukumar kula da harkokin sadarwa ta NCC da ta tabbatar cewa an bai wa masu amfadani da layukan zabin samun sakonnin bisa ra'ayin kansu ta hanyar saka wasu lambobi na musamman."

KU KARANTA KUMA: Dakarun NAF sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa

A wani labarin kuma mun ji cewa Gwamnatin kasar Najeriya, Nijar da Bini sun kafa kwamitin hadaka domin tattauna game da rufe iyakoki da Najeriya ta yi, tare da kokarin lalubo hanyar shawo kan matsalar, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kasashen uku sun kafa kwamitin hadaka daya kunshi Yansanda, hukumar yaki da fasa kauri da kuma hukumar kula da shige da fice na kasashen uku domin su gudanar da sintiri a kan iyakokin kasashen.

Kasashen sun amince da kafa wannan kwamiti ne bayan zaman tattaunawa da suka da juna a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja, inda ministan harkokin kasashen waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa kasashen sun lura da dukkanin korafe korafen da kowannensu ya gabatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel