Tirkashi: Mai gari yayi walankeluwa ya fada cikin kabari ya ce allan fur baza a binne wasu ma'aurata ba
- Wata dagacin kauye Ikot Uduak a karamar hukumar Calabar dake cikin jihar Cross River tayi tsalle ta fada cikin wani kabari yayin da ake yunkurin binne wasu ma'aurata
- Dagacin ta ce, ma'auratan ba 'yan asalin garin bane, lamarin da babban dan mamatan ya musanta
- Dagacin tace, matukar aka birnesu, ba shakka za ta kwakwalosu tare da banka musu wuta, su kone kurmus
Wata dagacin kauyen Ikot Uduak, da ke cikin karamar hukumar Calabar a jihar Cross River ta fada kabarin wasu ma'aurata a kauyen don hana a binne su.
Kamar yadda Daily Post ta ruwaito, dagacin kauye, mai martaba Efio-Awan Asuqo Asibon ta ce, ba za a binne ma'auratan masu suna Mr da Mrs Ekpe Okon Edet a kauyen ba saboda ba asalin 'yan garin bane.
Basset Okon Edet, daya daga cikin 'ya'yan ma'auratan da suka rasu, yayin bada bayanin lamarin, yace, "wannan gawarwakin iyayena ne kuma gidan nan kakana ne ya siya. Mahaifina Ekpe Okon Effiom ya ci gado. Muna da takardun yarjejeniyar filin,"
"Dagacin kauyen makwabciyar mu ce, ta so ta siyar da filin amma ta kasa saboda mahaifina yana raye, kuma ba ta yi wani yunkurin tashin sa ba. A nan ya rayu ya haifi yara 11 kuma a nan aka haifemu kuma muka girma."
KU KARANTA: An gano kauyuka 67 a Abuja da ake kashe tagwaye da zabiya da zarar an haife su
Ya ce, "Bayan rasuwar mahaifinmu, Asibong ta so kwace gidan, inda ta yanke wani bangare ta siyarwa wani mutumi ya gina wajen siyar da magunguna. Yanzu mun zo binnesu Asibong ta ce kada mu birnesu saboda ba nan ne asalinmu ba."
Dagacin kauyen Efio-Awan Asibong, kamar yadda rahoto ya sanar tace 'yan hayanta ne. Tayi bayanin cewa basu da takardun shaidar mallakar wajen. Ta yi alakwarin in har aka birne gawarwakin sai ta sa an konesu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng