Ba ta iya gamsar da mijinta ta fannin auratayya shiyasa na ke taimakonta – Yar aiki

Ba ta iya gamsar da mijinta ta fannin auratayya shiyasa na ke taimakonta – Yar aiki

Wata budurwa yar shekara 28 da ke aikatau, wacce uwargijiyarta ke zarginta da aikata zina da maigidanta ta bayyana cewa, ko daya ita ba ta aikata laifi da ake tuhumarta akai da nufin kuntatawa uwardakin tata ba.

A cewarta alfarma ta yiwa uwardaki tata ta hanyar killace mijin nata daga yawon bin matan banza, sakamakon rashin gamsar dashi da matar tasa bata iya yi.

Mai aikin wacce aka ambata da suna Keith Gaye ta sanarwa kotun Accra na kasar Ghana cewa a iya lokacin da ta dauka tana zama da su a gidan, ta san irin hali da maigida ke ciki na rashin gamsar dashi da matar tasa bat a iya yi, wanda hakan ne ya sanya shi neman taimakon ta.

Don haka tace babu abunda za ta iya yi domin kyautatawa uwardakin tata da ya wuce amsar tayinsa domin kare mata shi daga bin matan banza.

Tun da farko dai mai karar ta zargi ’yar aikin ne da satar kudi a lokacin da ta gan ta ta shiga dakin maigidan, kafin ya yi tafiya, amma bayan tafiyar tasa sai a ka wasu kudi a ciki. Ganye ta ce, ko kadan ba maganar kudi ce ta kai ta wajen maigidan ba, domin ita ba mutuniyar banza ba ce ballantana ta yi satar kudin da ba nata ba, illa kawai ita mai taimako ce, don ta tserar da aurensu.

KU KARANTA KUMA: Mijin mace 1: Ba zan taba yiwa matata Maimunatu kishiya ba – Ali Nuhu

Jin kalaman bakin Ganye ya sanya kotun ta tsaya cak, inda hatta mai gabatar da kara ya rasa irin tambayoyin da zai cigaba da yi ma ta.

Ita kanta mai karar ta rasa abinda za ta ce, illa kuka kawai ta ke faman rusawa. A nan ne alkalin kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci da za ta sanar da lauyoyi a nan gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel