An tura dan majalisa gidan yari saboda dukan wata mata

An tura dan majalisa gidan yari saboda dukan wata mata

Alkali ya bukaci a adana masa wani dan majalisa a gidan yari akan zarginsa da ake da dukan wata mata tare da yi mata tsirara. Wanda ake zargin mai suna Uduak Nseobot asalin dan karamar hukumar Ibiono Ibom ne na jihar Akwa Ibom.

Gwamnatin jihar ce ta gurfanar da Nseobot a gaban kotu a kan zarginsa da ake da garkuwa da mutane, cin zarafi da kuma yi wa wata mata mai suna Iniubong Essien tsirara, wacce ya zarga da satar masa wasu kudade.

Nseobot yace, an musu liki da kudin ne a wani biki.

Da farko an gurfanar dashi ne tare da matarsa, Aniedi, wacce ke rayuwa a Amurka. Daga baya ne aka wanke matar don samun damar gurafanar da mijin yanda ya dace.

Jastis Archibong Archibong na babbar kotun Uyo a ranar Alhamis, ya yi watsi da sukar farko da lauyan wanda ake kara, Mfon Ben, ya yi.

DUBA WANNAN: Dalilin sauke mataimakin kakakin majalisar jihar Gombe

Mai shari'ar ya umarci da a tsare masa Nseobot a gidan yari, bayan da ya musanta laifukansa.

An dage sauraron karar zuwa 27 ga watan Nuwamba inda kotun zata duba bukatar bada belin wanda ake zargin.

Matar da abun ya faru da ita, Essien, tace ita kawar matar dan majalisar ce tun kusan shekaru 10 da suka gabata. Essien ta musanta satar kudin.

Ta sanar da jaridar Premium Times cewa, ta taimakawa su Nseobot wajen girki da karrama baki amma ba ita ba ce ta taimaka wajen kwashe kudin liki.

Nseobot da matarsa, sun samu tallafin wasu abokansu, inda suka sace Essien daga gidanta da sassafe a watan Nuwambar shekarar da ta gabata. Sun boyeta a wani kauye da ke da nisan kilomita 27 tsakaninsu da garinsu.

"Sun yi min duka sannan suka tilasta ni tafiya tsirara a kauyen. Sun cire min kayana, rigar nono da dan kamfai," Essien wacce ta fi shekaru 40 ta sanar da jaridar Premium Times.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel