Bincike: An gano cewa gajerun mutane sun fi dogayen mutane shiga damuwa a duniya

Bincike: An gano cewa gajerun mutane sun fi dogayen mutane shiga damuwa a duniya

- Bincike ya nuna cewa, rashin tsayi ko gajarta na sanya wasu irin tunane-tunane a zuciyar mutane

- An gano hakan ne kuwa sanadin binciken da wasu masana da suka gudanar akan mutanen

- An gano cewa, tsayi na taka rawar gani wajen sakawa mutum kwarin guiwa, tunani akan cutarwar mutane, kaskanci ko daukaka da sauransu

Bari mu fara da tambaya, shin mai karatu ya taba yin karya akan tsawonsa?

Akwai tabbacin hakan ba sabon abu bane. Tsawon mutum, idan ya dangantasa da na sauran mutanen da yake rayuwa dasu, jigo ne ga yanda kake kallon kanka da rayuwarka, saboda haka tsawo yana da mutukar muhimmanci. Amma me kimiyya ta ce akan tsawo da kuma taka rawar da yake a tunanin mutum?

Kamar yanda binciken da aka yi a shekarar 2014 ya nuna cewa tsawon mutum kan bashi tunanin tsare kansa sakamakon yunkurin mutane na cutar da shi.

Masu bincike Daniel Freeman, Nicole Evans, Rachel Lister, Angus Antley, Mel Slater da Graham Dunn sun gwada bincikensu akan wasu mutane. Sun bukaci mutanen da su yi tafiya a motar haya, inda daga baya suka bayyana yanda suke ji a zuciyarsu.

Sun kara tafiya a motar hayan amma sun zauna ne ta yadda wani yafi wani tsawo amma da gangan. Hakan kuwa ya kawo musu tunani daban-daban a zukatansu, sakamakon banbancin tsayinsu.

KU KARANTA: Innalillahi: Matashin saurayi dan Najeriya ya shake mahaifiyarsa har sai da ta mutu

Mutanen da tsayinsu ya ragu, sun bayyana cewa, sun ji kaskanci, sun zama koma baya da rashin kwarin guiwa sakamakon rage musu tsayi da aka yi. Duk da kuwa ba a sanar musu cewa an rage musu tsayin ba.

Daya daga cikin fasinjojin ya bayyana yanda ya lura cewa, sauran fasinjojin na masa gatsali duk da kuwa a gaskiyar lamarin ba haka bane.

Amfanin wannan binciken shine, gano yadda gajeru da masu tsayi ke kallon kansu, yanda suke ji; kaskanci ko daukaka.

A takaice dai wannan binciken na nuna cewa, gajarta na cirewa mutum kwarin guiwa hakazalika tsayi na saka izza. Hakan zamu iya ganinsa a yanda gajeru ke da matukar fadin rai wanda suke tunanin zai dawo musu da izzarsu, kuma yasa mutane su mutunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng