Inda ranka ka sha kallo: Mutumin da ya yi aure sau 60 a shekaru 25 ya shiga hannun Yansanda

Inda ranka ka sha kallo: Mutumin da ya yi aure sau 60 a shekaru 25 ya shiga hannun Yansanda

Rundunar Yansandan kasar Bangladesh ta kama wani mutumi dan shekara 45 mai suna Abu Baker sakamakon kararsa da matarsa ta shigar gaban Yansanda inda take zarginsa da aure sau 60 a cikin shekaru 25.

Shi dai Abu Baker malamin makaranta ne, kuma Da ne ga Badshah Mia dake kauyen Shobharchar dake yankin Goyalerchar cikin lardin Jamalpur na kasar Bangladesh, kamar yadda jaridar DhakaTimes ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnan Borno ya sanya ma makafi, kurame da guragu 3,127 albashin dubu Talatin-talatin

A ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba ne Yansanda suka kama Abu Baker wanda ake yi ma inkiya da ‘Baker Teacher’, wanda Yansanda suka bayyana cewa ya yi aurensa na fari tun yana dan shekara 20.

“Ya yi aure sau 60 zuwa yanzu da yake da shekaru 45, kuma yana amfani da takardun bogi ne wajen shirya wadannan aure aure, inda a wasu takardun yake nuna bai taba aure ba, a wasu kuma ya nuna matarsa ce ta mutu.” Inji Yansanda.

Matar ‘Baker Teacher’ ta sittin, Rosy Khanum ce ta tona masa asiri bayan ta kai ma ofishin Yansanda dake Purbadhala kararsa bayan ya aureta a watan Agusta da takardun bogi, inda ya yi amfani da sunan karya; Shaheen Alam, dan Akram daga kauyen Kutuberchar.

Bayan ya auri Rosy, sai ya nemi mahafinta ya biyashi sadakin Tk2 lakh, kimanin N853,264 a kudin Najeriya, amma mahaifinta ya ki amince, daga nan sai ya sace ma mahaifin nata Tk80,000, kimanin N341,305 ya tsere.

Sai dai Baker Teacher yace duk da cewa sau 60 yana aure, amma yaransa 7 kacal, kuma auren jari kawai yake yi, daga baya sai ya saki matan. A yanzu haka dai Baker yana tare da matarsa ta farko Sazeda Begum da wasu mata biyu, da yaransa bakwai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel