Bidiyo: Wani Kirista ya kone Bible ya ce babu wani abu a cikin littafin sai karya

Bidiyo: Wani Kirista ya kone Bible ya ce babu wani abu a cikin littafin sai karya

- Bidiyon wani mutum dan kasar Ghana na ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani

- Bidiyon ya nuna yadda mutumin ya yayyaga shafukan littafin Bible tare da banka musu wuta

- Ya zargi addinin kiristancin da damfarar mutane tare da sauya musu tunani

Wani bidiyo na wani mutum dan kasar Ghana na ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani. Bidiyon ya nuna yadda mutum ya yayyaga littafin Bible tare da kone shi kurmus, mutumin ya ce an dasa wa kiristoci tunanin cewa littafi ne mai tsarki bayan ba haka abin yake ba.

Kamar yadda mutumin da ba a san ko waye ba ya bayyana, ya gaji da yarda da ubangiji tare da littafin Bible din. A don haka ne ya yanke shawarar kona shi.

A surkullen da yayi da yarensa, mutumin ya nuna damuwarsa yayin da yake yaga shafukan bibul din, inda daga baya ya banka masa wuta.

KU KARANTA: Babbar magana: Ban san uban me mahaifina yake yi ba har su Dangote suka yi kudi suka barshi - Tonto Dikeh

Wannan abu da yayi haramun ne a ka'idar addinin kirista, amma mutumin ya nuna fushinsa da bacin ransa akan dukkan addinin kiristancin.

A wani bidiyo shima da ya dinga yawo a kafafen sada zumunta, an nuna fasto yana ciyar da mutane shafukan bibul a coci.

Bidiyon ya nuna faston yana yaga bibul din, inda daga baya ya ba mutanen da ke cocin don su ci. Tuni mutane suka dinga suka tare da Allah wadai da wannan dabi'a ta wadannan mutanen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel