Ya kashe wani da ke binsa bashi bayan fada ya kaure a tsakaninsu a jihar Niger

Ya kashe wani da ke binsa bashi bayan fada ya kaure a tsakaninsu a jihar Niger

- Jami'an yan sandan jihar Niger sun kama Wani mutum mai suna Saidu Mohammed na kauyen Gbogan Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu na jihar kan zargin kisan kai

- Marigayin dai na bin Saidu bashin wasu kudade inda ya hana shi kudin nasa

- Mai laifin ya dauki marigayin ya tika shi da kasa inda hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar

Rundunar yan sandan jihar Niger a ranar Lahadi, ta tabbatar da kama Wani mutum mai suna Saidu Mohammed na kauyen Gbogan Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu na jihar kan zargin kisan kai.

An tattaro cewa wanda ake zargin ya kashe wani Bala Yahaya a wannan kauyen ya hanyar tika shi da kasa biyo bayan wani rikici da ya shiga tsakaninsu ta sanadiyar bashi.

An rahoto cewa mahaifin wanda abun ya ritsa da shi, Mallam Yahaya ya bayyana cewa dansa ya je kasuwar Gbogan domin karbo wani bashi daga hannun wanda ake zargin, wanda ya ki biyan bashin.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a lokacin da marigayin ya je karbo kudinsa daga wajen mai laifin, sai fada ya kare a tsakaninsu.

Sai mai laifin ya dauki marigayin ya tika shi da kasa. Hakan ne ya yi sanadiyar mutuwar Bala yayinda ya yanke jiki sannan aka yi gaggawan kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

An tattaro cewa wanda ake zargin ya amsa cewar marigayi na binsa bashin wasu kudade da kuma fadar da ya shiga tsakaninsu wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Ya yi bayanin cewa ya fusata ne shiyasa har ya yi fada da marigayin domin ya tambaye shi kudinsa cikin tijara.

Kakakin yan sandan jihar Muhammad Abubakar ya tabbatar da lamarin cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa.

KU KARANTA KUMA: Assha: Masu garkuwa da mutane sun kashe wani dan kasuwa bayan sun karbi kudin fansa a jihar Nasarawa

Abubakar ya ce an kai marigayin babban asibitin Mokwa inda aka tabbatar da mutuwarsa, inda ya kara da cewa an shigar da lamarin kotu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel