An kai hari gidan casun Saudiyya

An kai hari gidan casun Saudiyya

Jami'an tsaro a kasar saudiyya sun cafke wani mutum da ya sokawa 'yan wasan rawa guda uku wuka yayin da suke baje kolin nishadinsu a dandalin rawa na Sarki Abdullahi.

An bayyana cewa, 'yan rawar sun samu rauni a harin da ya auku a dandalin casun da ake gudanarwa a Riyadh don nishadi, lamarin da ya haramta a baya a kasar ta Saudiyya, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Wani bidiyo na yawo a kafafen sadarwar ya nuna yadda 'yan rawar ke cashewarsu sanye da tufafi masu walwalin zinari, sai kawai ba zato balle tsammani, wani mutum ya zaro sharbebiyar wuka mai tsawon santimita 30 ya aukawa tawagar da ke nishadantarwa a dandalin.

Babu jimawa mutumin ya zame ya fadi kasa inda jami'an tsaro suka hanzarta cafkesa.

DUBA WANNAN: Har yanzu ni ne gwamna - Gwamnan PDP da kotu tace an tafka magudi a zabensa

Maza biyu da mace daya ne maharin ya raunata da wukar amma ance raunin ba mai tsanani ba ne.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayyana cewa, maharin yana da shekaru 33 a duniya kuma dan kasar Yemen ne. Ba a sanar da manufar ba ko dalilin harin nasa.

Maharin ya kai farmakin ne a dandalin Sarki Abdullahi ne kuma bikin na daya daga cikin casun da aka dau watanni biyu ana gudanarwa.

Hukumomin kasar sun ce suna sa ran samar da kudin shiga har dala biliyan 64 ta bangaren nishadi don rage dogaro a kan ma fetur.

Sauye-sauyen da suka samu kasar sun hada da bude gidajen sinima tare da hada casun da manyan mawaka zasu halarta da kuma shirya damben zamani na maza da mata. An ba mata damar tukin mota a kasar tare da damar kama dakin otal. hakan kuwa ya fusata wasu malaman kasar amma kuma matasan kasar sun yi maraba da sabon salon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel