Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Yan Boko Haram sun sako wani limamin coci da dalibar makaranta

Zakaran da Allah Ya nufa da cara: Yan Boko Haram sun sako wani limamin coci da dalibar makaranta

Mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram sun sako wani babban limamon cocin Living Faith dake garin Maiduguri mai suna Moses Oyeleke mai shekaru 58, tare da wata dalibar makaranta, Ndagiiya Ibrahim Umar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito Allah Ya kubutar da mutanen biyu ne ta hannun wasu kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu, Kalthum Foundation for Peace da Initiative for Peace Bullding Movement da suka dauki tsawon lokaci suna tattaunawa da kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a wajen daurin aure, mutum 1 ya mutu

Yan ta’addan sun sace faston ne a watan Afrilun shekarar 2019 tare da wani dan bautan kasa mai suna Abraham Amuta yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Chibok domin kai musu kayan agaji daga cocinsu.

Sai dai har yanzu kungiyar bata saki dan bautan kasan ba, amma faston ya sha da kyar bayan kwashe watanni 7 a hannunsu. A cewar Faston: “Muna kan hanyarmu ta zuwa Chibok ne a lokacin da suka kama mu, daga nan suka kai mu har Sambisa.

“Sun bamu tabbacin idan har suka kammala tattaunawa da kungiyoyin zasu sako dan bautan kasar tare da yayar wannan yarinyar da suka sako mu tare, zuwa watan Disamba.”

Ita kuwa Ndagiliya cewa ta yi watanninta 9 a hannun Boko Haram tun bayan da suka dauketa daga wata makaranta dake karamar hukumar Askira Uba tare da yayarta da kuma wasu wadanda har yanzu suna hannunsu. Sai dai guda daga cikin masu tattaunawa da kungiyar yace babu ko sisi da suka biya.

Mataimakin gwamnan jahar Borno, Usman Kadafur ne ya karbi bakoncin faston da yarinyar a fadar gwamnatin jahar Borno dake garin Maiduguri, kuma ya tabbatar da zasu mikasu zuwa asibiti domin likitoci su duba lafiyarsu.

Daga karshe mataimakin gwamnan ya mika godiyarsa ga duk wadanda suka bada gudunmuwa wajen sako su, musamman kungiyoyin biyu tare da jami’an tsaro, sa’annan ya bada tabbacin gwamnatin Borno za ta cigaba da daukan matakin sulhu da yan ta’addan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel