Sheƙau ya aikowa da ma'abota maulidi sako cikin wata sabuwar bidiyo

Sheƙau ya aikowa da ma'abota maulidi sako cikin wata sabuwar bidiyo

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar 'yan ta'addar Boko Haram ya fitar da wani faifan bidiyo na tsawon mintuna 33. Shugaban 'yan ta'addan ya musanta sahihancin bikin Maulidi a musulunci.

Bidiyon mai tsawon mintuna 33 ya nuna yadda shugaban ke rike da wasu takardu yana karantowa cewa babu wata hujja ko ittifaki na malamai a kan lokacin da aka haifi manzon Allah, annabi Muhammad SAW kamar yadda fitaccen dan jarida da ya saba sharhi a kan Boko Haram, Ahmad Salkida ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Kusan shekaru 20 kenan da 'yan ta'addan suka gallabi kasar nan. Sunyi sansani ne a dajin Sambisa dake jihar Barno amma suna sa 'yan kungiyar a sashi daban-daban na kasar nan.

DUBA WANNAN: Wasu abubuwa 5 da jama'a basu sani ba a kan Mamman Daura

Kullum ikirarin kungiyar ta'addancin Boko Haram shine a ajiye kundin tsarin mulkin kasar nan a rungumi Kur'ani da Hadisi don su zama alkibla a mulki, zamantakewa, shari'a, ilimi, kasuwanci da sauran lamurran yau da kullum na al'umma.

Rashin aminta da hakan ne kuwa yasa suka dau alwashin ba zasu yada makamansu ba har sai sun ga abinda ya turewa buzu nadi.

Idan ba zamu manta ba, kungiyar ta'addancin ta musulunci sunyi sansaninsu ne a yankin Arewa maso gabas din kasar nan da kuma wani yanki na kasashen Kamaru, Chadi da Nijar.

'Yan ta'addan sun yi nasarar fatattakar mutane a kalla miliyan 2.3 daga gidajensu a yankin. Sun kware ne a take hakkin dan adam wadanda suka hada da garkuwa da mutane, safarar mutane da kuma kunar bakin wake.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel