Tashin hankali: Wata giwa da aka saka wa suna 'Osama bin Laden' ta kashe mutane 5 a cikin sa'a 24

Tashin hankali: Wata giwa da aka saka wa suna 'Osama bin Laden' ta kashe mutane 5 a cikin sa'a 24

Wata giwa da aka saka wa sunan tsohon shugaban kungiyar Al-Qaed, marigayi Osama bin Laden, ta kashe mutane biyar a wani kauyen kasar Indiya, kafin daga bisani jama'a su yi taron dangi domin kama dabbar, kamar yadda rahotanni daga kasar suka bayyana a ranar Litinin.

Ma'aikatan hukumar raya gandun daji sun yi amfani da na'urori na musamman da ke shawagi a sararin samaniya da kuma wasu Giwayen gida kafin su samu nasarar kama Giwar da mazauna jihar Assam, da ke arewa maso gabashin kasar Indiya, ke kira da 'Laden'.

"Yau ma, kamar yadda muka saba a 'yan kwanaki biyun da suka gabata, mun fito farautar Giwar. Mun yi amfani da wata allura, da ake harba wa dabbobi domin ta kashe musu jiki, a kan Giwar bayan mun gano ta," wani babban jami'in hukumar raya gandun dajin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sannan ya cigaba da cewa, "yanzu babban aikin da ke gabanmu shine yadda zamu dauki Giwar zuwa wani jejin da babu mutane."

DUBA WANNAN: Ba na maraba da karuwai a masarauta ta - Babban Sarki a arewa

Dabbar ta kashe mutane biyar, da suka hada da mata uku, yayin wani kutse da ta yi na tsawon sa'a 24 a yankin Goalpara a cikin watan Oktoba.

Jami'an hukumar sun tabbatar da cewa zasu kula da hakkin dabbar da walwalar ta da kuma tsaron lafiyar jama'a kafin su yanke shawarar wurin da zasu mayar da ita.

Kimanin mutane 2,300 ne giwaye suka kashe a kasar Indiya a cikin shekaru biyar da suka wuce, kamar yadda alakaluman hukuma suka bayyana a watan Yuni.

Yawaitar al'umma na kara jawo tsukewar gandun daji da dabbobi ke zaune a kasar Indiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel