Shin wanene Farfesa Tam David West wanda ya rasu yau a 83

Shin wanene Farfesa Tam David West wanda ya rasu yau a 83

A yau dinnan, Litinin, 11 ga Watan Nuwamban 2019, mu ka samu labarin rasuwar Farfesa Tam David West. David West fitaccen Masani ne kuma tsohon Minista a Gwamnatin tarayya a 1985.

Kusan Marigayi David–West shi ne kadai Ministan da aka tuhuma da laifi a gwamnatin Janar Ibarahim Babangida. A 1991, kotu ta wanke Farfesan daga duk wani zargin da ake jefe sa da su.

Mun kawo kadan daga cikin tarihin Marigayin domin wadanda ba su san labarinsa ba.

1. Haihuwa

A cikin Watan Agustan 1936 aka haifi Tam David-West ne a Garin Buguma, da ke cikin Yankin Kalabari, wanda yanzu ta ke jihar Ribas. Ya rasu ya na da shekaru 83 da kwanaki kusan 75 a Duniya.

2. Karatu

Marigayin ya fara karatunsa ne a gida a Jami’ar Ibadan a 1956. Kamar yadda mu ka tsakuro, Marigayin ya samu shaidar Digirin farko a 1958 a Jami’ar jihar Michigan ta Amurka. A 1960 ya garzaya Yale ya yi Digiri na biyu. Zuwa 1966 David West ya samu PhD a Jami’ar McGill ta kasar.

3. Aiki

Bayan ya kammala Digirin farko zuwa na uku a cikin shekaru 10 rak, sai aka dauki David-West aiki a matsayin babban Malami a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo. A 1975 ne aka yi masa karin matsayi zuwa Shehi watau Farfesa bayan shekaru 6 ya na kowar da ilmin halittun ‘Virus’

KU KARANTA: Dangi sun yi magana game da rashin lafiyar Abdulrasheed Maina

4. Gwamnati

Farfesa Tam David-West ya shiga gwamnati inda ya yi aiki a matsayin Kwamishinan jihar sa ta Ribas daga 1975 zuwa 1979. Haka zalika ya na cikin wadanda su ka tsara kundin tsarin mulkin Najeriya na 1979. An yi wannan ne a lokacin mulkin Sojin Marigayi Janar Murtala Muhammed.

5. Minista

Bayan dawowar mulkin Soja a Najeriya, gwamnatin Janar Muhammadu Buhari ta nada David West a matsayin Ministan man fetur. Bayan hambarar da wannan gwamnati, aka maida shi Ministan karafuna da mahakai. Daga baya aka sauke shi bisa zargin kawowa Najeriya matsala.

6. Siyasa

Bayan ya fita daga gwamnati, David-West bai shiga cikin harkar siyasa tsundum ba, amma ya rika tsoma bakinsa kan sha’anin kasa. David-West ya soki gwamnatocin baya amma bai da jam’iyya.

7. Rubuce-rubuce

Marigayi Farfesa Tam David-West ya na cikin wadanda su ka yi rubuce-rubuce domin wanke Muhammadu Buhari daga zargi da sukar jama’a. Daga cikin littattafan da ya rubuta a kan Buhari akwai ‘16 sins of General Muhammadu Buhari’ da kuma ‘Who is really Muhammadu Buhari.”

Sauran litattafai da takardun da Marigayin ya gabatar sun hada da:

- Of politics and education

- Philosophical essays

- Educational planning and policy

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel