Manyan masu kudi mata 10 a Najeriya
Idan aka yi maganar dukiya a Najeriya, ba a cika kiran sunan mata ba. An fi kiran sunanayen maza a matsayin manyan masu kudi. Idan kuwa aka fara zancen mata masu kudi a kasar nan, sunan Folorunsho Alkija kadai ake kira.
Zamu gabatar muku da manyan mata masu kudi a Najeriya da ba a jin sunayensu a kanun labarai amma sun mallaki biliyoyin nairori.
1) Folorunsho Alajika
Itace mace mafi arziki a nahiyar Afirka kuma ba shakka ya zama dole ta shiga wannan lissafin duk da sananniya ce. 'yar kasuwa ce kuma mai hannayen jari a kasuwar man fetur, kyale-kyale da harkar gidaje. Arzikinta ya ka $1billion a 2019.
2) Bola Shagaya
Hajia Bola Shagay ita ma babbar 'yar kasuwa ce a a duniyar kasuwancin Najeriya. 'Yar kasuwar mai shekaru 60 a duniya ta fara aiki ne a bangaren kididdigar kudi a babban bankin Najeriya. Daga baya ta zama babbar manajar kamfanin Practoil Limited, daya daga cikin manyan kamfanoni masu shigowa tare da rarrabe man fetur a Najeriya. Tana da arzikin da ya kai $900 million.
3) Bimbo Alase-Arawole
Bimbo Alase wata shahararriyar mai arziki ce a Najeriya. Ta kafu ne sakamakon kasuwanci da ta tsunduma ciki. Itace wacce ta kirkiro kamfanin Leatherworld, babban kamfani kayan daki ne. Tana da arzikin da ya kai $400million.
4) Fifi Ejindu
Fifi Ekanem Ejindu mace mai zanen gidaje kuma 'yar kasuwa. Matar mai shekaru 57 wacce ake kira da Fifi Ejindu ce shugabar Building Support systems kuma da tana da babban kaso a Starcrest Group of Comapanies. Arzikinta ya ka $300million.
Fifi Ekanem Ejindu is a Nigerian Architect, businesswoman and philanthropist.
DUBA WANNAN: Zuwa kotu a keken guragu: Iyalin Maina sun fadi gaskiyar halin da lafiyarsa ke ciki
5) Daisy Danjuma
Sanata Daisy Ehanire Danjuma ta kammala karatun jami'arta a fannin shari'a daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Tana da gogewar aiki na sama da shekaru 40. ta fara aiki ne a jiharta.
Daisy Danjuma ce mataimakiyar shugabar kamfanin South Atlantic Petroleum, wani kamfanin man fetur wanda ke samun miliyoyin daloli a matsayin kudin shiga. Itace shugabar babban kamfanin maganin nan na May and Baker Nigeria Plc.
6) Stella Chinyelu Okoli
Stella Okoli dan najeriya ne da ta karanci fannin hada magunguna kuma 'yar kasuwa ce. Itace shugaba kuma mamallakiyar kamfanin Emzor, daya daga cikin manyan kamfanoni hada magunguna a najeriya. Tana da arzikin da ya kai $500million.
7) Mo Abudu
an fi saninta da Mo Abudu, daya daga cikin manyan 'yan kasuwar najeriya da ake girmamawa idan aka zo duniyar yada labarai. tayi suna ne har da ta fuskar arzikinta. Itace mamallakiyar Ebonylife TV da EbonyLife studios. Arzikinta ya kai $10million.
8) Diezani Alison-Madueke
Wannan itama babbar mai kudi ce a jerin matan Najeriya kuma tayi suna ne a bangaren siyasa. An zabeta ministar man fetur ta Najeriya ne a ranar 26 ga watan Yuli 2007. Duk da a halin yanzu ana tuhumarta da almubazzaranci amma ta samu damar shiga jerin kasaitattun matan nan. Tana arzikin da ya kai biliyoyin daloli.
9. Ngozi Okonjo-Iweala
Idan za ayi magana akan hazaka, toh tabbas sunan Ngozi zai shigo a jerin mata sakamakon nasarorin da ta samu a aikinta. Kwararriya ce a fannin tattalin arziki wacce ta yi ministar kudi. Ta samu gogewa a bangaren habaka tattalin arziki a bankin duniya na kusan shekaru 25.
Itama daraktar tuwita ce mai zaman kanta tun a 2018 kuma tana da arzikin da ya kai $5million.
10) Stella Oduah-Ogiemwonyi
Stella Oduah-Ogiemwonyi itace ta karshe amma ba karama a jerrin matan nan. Stella sanatar Najeriya ce kuma tsohuwar ministar sufurin jiragen sama ta kasar nan. Tana da arziki da ya kai $300million.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng