Dangote ya fara aikin kafa masana’antar shinkafa a Kebbi - Gwamna Bagudu

Dangote ya fara aikin kafa masana’antar shinkafa a Kebbi - Gwamna Bagudu

Mun samu labari daga jaridar Vanguard cewa Mai girma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya jinjinawa Kamfanin Dangote na shirin da ya ke yi na kafa Masana’antar casa da gyaran shinkafa.

Rahotannin sun bayyana cewa Sanata Atiku Bagudu ya ce wannan masana’anta da za a bude a jihar ta Kebbi za ta bunkasa tattalin arzikin jihar tare da kawowa hanyoyin samun aikin yi.

Bagudu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ziyarci Yankin Saminaka da ke karamar hukumar Shanga inda za a gina wannan kamfani da zai taimakawa noman shinkafa a fadin jihar.

Gwamnan ya fitar da jawabin kewayen da ya je ne ta bakin Sakatarensa na yada labarai, Malam Abubakar Dakingari. Dakingari ya yi wannan jawabi ne a Ranar Lahadi, 10 ga Watan Nuwamba.

Abubakar Dakingari ya ke cewa a lokacin da gwamnan da kuma wasu manyan jami’an gwamnatin jihar su ka kewaya, ana kokarin kafa manyan dakunan adana shinkafa 32 a kamfanin.

KU KARANTA: Najeriya za ta fara fita da shinkafa – Kamfanin Dangote

Malam Dakingari ya rahoto gwamnan ya na cewa “Dole mu yabawa kokarin da kamfanin Dangote ya ke yi, musamman Alhaji Aliko Dangote, wanda ya fara kawo wannan aiki zuwa jihar Kebbi.”

Mai girma gwamnan ya kara da cewa: “Wannan kamfani zai taimaka sosai wajen rage matsalar rashin aikin yi a wajen Matasa, tare da bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma Najeriya baki daya.”

Bayan haka kuma gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen karkato da hankalin masu zuba hannun jari su shigo jihar Kebbi su kafa irin wadannan kamfanoni da za su kawo masu abin yi.

Duk a karshen makon na jiya, gwamnan ya karasa zuwa wani karamin kamfani aikin shinkafa da ke cikin Garin Yawuri a jihar ta Kebbi inda ya zanta da Mata da ke aikin shinkafa a kamfanin.

Jawabin ya ce wadannan mata sun bayyanawa gwamnan cewa farashin shinkafa ya fara yin kasa. A cewarsu, hakan ya nuna cewa tsare-tsaren gwamnatin tarayya sun fara aiki a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel