Bafulatani ya kashe dan uwansa saboda yana zarginsa da kwanciya da matarsa

Bafulatani ya kashe dan uwansa saboda yana zarginsa da kwanciya da matarsa

Wata kotun majistri dake zamanta a jahar Kwara ta bayar da umarnin garkame wani matashi bafulatani, Iliyasu Abubakar a kurkukun gwamnatin tarayya dake garin Ilorin saboda tuhumarsa da ake yi da halaka dan uwansa.

Jaridar Punch ta ruwaito ana tuhumar Iliyasu da kashe yayansa mai suna Isah ne a cikin wani daji dake rugar Fulani ta Gwanara cikin karamar hukumar Baruten na jahar Kwara bayan ya zargeshi da kwanciya da matarsa.

KU KARANTA: Wani mutum mai yara 23 ya yi cinikin dansa a kan kudi naira miliyan 5 a Nassarawa

Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Sanni Abdullah ya shaida ma kotun cewa laifin da ake tuhumar Iliyasu ya saba ma sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Kwara.

Dansandan ya bayyana ma kotun cewa mahaifin mutanen biyu, Malam Umaru Abubakar ne ya kai rahoton lamari ga ofishin yansanda dake Gwanara, inda daga nan aka mika maganan zuwa ga sashin binciken manyan laifuka na rundunar Yansanda domin gudanar da binciken sirri.

Malam Umaru ya kai ma yaransa ziyara a rugar domin ganin da suke ciki ne, amma sai ya tarar babu kowa a wajen sai shanunsu, daga nan sai ya bazama neman inda suka shiga, a haka ya gano gawar Isah dauke da sara a wuyarsa, amma bai ga kaninsa ba.

Bincike ya nuna bayan Iliyasu ya kashe dan uwansa ne sai ya tsallake zuwa jahar Oyo, amma Yansanda sun samu nasarar kamashi, kuma ya amsa laifinsa na kashe Isah, sai dai yace ya yi hakan ne saboda yana neman matarsa.

Iliyasu ya tabbatar ma Yansanda cewa Isah ya taba tabbatar masa da cewa shi ya dirka ma matarsa ciki har ta haifi dan da ta haifa mai shekaru 3 a yanzu, amma duk da gargadin da ya yi masa, Isah bai daina neman matarsa ba, wannan shi ne dalilin da yasa ya halakashi.

Sai dai Dansanda Sanni ya nemi kotu ta garkame Iliyasu saboda kotun ba ta da hurumin sauraron karar, daga bisani Alkalin kotun, Jumoke Bamigboye ta amince da bukatar Dansandan, ina ta bada umarnin garkame Iliyasu, tare da dage sauraron karar zywa ranar 26 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng